fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Tag: Colombia

Mutane 2 zuwa 3 ne ke Musulunta a kowanne mako a kasar Kolombiya

Mutane 2 zuwa 3 ne ke Musulunta a kowanne mako a kasar Kolombiya

Uncategorized
A kasar Kolombiya da ke Kudancincin Amurka, mutane 2 zuwa 3 ne ke Musulunta a kowanne mako.     Shugaban Cibiyar Al-Kurtubi da ke Bogota Babban Birnin Kolombiya Ilyas Marzuki ya bayyana cewar "Akwai mutane da yawa da suka karbi Musulunci a nan. A kowanne mako a Kolombiya mutane 2 zuwa 3 ne suka Musulunta. Mafi yawansu daliban Kolombiya ne. Kaso 70 zuwa 80 na jama'armu daga baya suka shiga Musulunci."   Marzuki ya ci gaba da cewar mafi yawan masu zuwa Masallacin Juma'a na Imam kurtubi 'yan shekaru 15 zuwa 40 ne da suka zabi shiga Addinin Musulunci. TRThausa.