fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Tag: Copa Italia

Coppa Italia: Inter Milan suna gunadar da atisayi domin daukar fansa anjima tsakanin su da Napoli

Coppa Italia: Inter Milan suna gunadar da atisayi domin daukar fansa anjima tsakanin su da Napoli

Wasanni
Inter Milan sun cigaba da gudanar da atisayi gami da wasan na biyu na Semi final da zasu buga anjima da karfe takwas tsakanin su da Napoli, yayin da yan wasan Antonio Conte suke harin rama kwallon da Napoli suka ci su a wasan farko. A cigaba da buga wasannin kasar Italia bayan cutar korona tasa an dakatar da wasannin har na tsawon watannin hudu. Inter sun shirya rama kwallon da Fabian Ruiz ya ci su a wasan farko yayin da zasu buga wasan ba tare da yan kallo ba. Yan wasan Antonio Conte zasu yi tafiya izuwa Naples domin su kara da Napoli a wasan na biyu na Semi final, yayin da Juventus suka cancanci buga wasan karshe na gasar Coppa Italia a daren jiya saboda kwallon da suka ci wadda ba ta gida ba.
Juventus sun cancanci buga wasan karshe na gasar Coppa Italia bayan tashi 0-0 tsakanin su da AC Milan

Juventus sun cancanci buga wasan karshe na gasar Coppa Italia bayan tashi 0-0 tsakanin su da AC Milan

Wasanni
A yau ranar 12 ga watan yuni aka cigaba da buga wasannin gasar Coppa Italia yayin da Juventus suka kara da AC Milan bayan an dakatar da gasar watanni uku da suka gabata saboda annobar cutar coronavirus. Juventus sun cancanci buga wasan karshe na gasar wanda za'a buga ranar laraba saboda sun yi nasarar tashi a 1-1 a wasan farko da suka buga na semi final, kuma zasu kara da Napoli ko Inter Milan a final din, yayin da suma Napoli da Inter zasu buga wasan nasu gobe. Juventus sun samu babbar dama a wasan yayin aka basu penariti a minti 16 na wasan, Amma Ronaldo ya barar da kwallon. Bayan dakika shida kuma aka ba dan wasan gaba na AC Milan Ante Rebic jan kati saboda ya yiwa Danilo bugun keta. Duk da haka dai sai da suka tsorata Juventus yayin da suma kusa jefa kwallo guda amma yan...
Kasar Italia zasu ci gaba da buga wasannin su na Coppa Italia daga ranar 12 ga watan yuni

Kasar Italia zasu ci gaba da buga wasannin su na Coppa Italia daga ranar 12 ga watan yuni

Wasanni
Ministan wasanni na kasar Italia Vincenzo Spadafora ya tabbatar da cewa za'a cigaba da buga wasannin kasar daga ranar 12 ga watan yuni yayin da za'a buga wasannin kusa da karshe na gasar Coppa Italia (semi final). An buga wasan farko na semi final din a watan febrairu yayin da Juventus suka kara da Ac Milan a filin San Siero kuma suka tashi 1-1, sai kuma nasarar da Napoli suka yi tsakanin su da Inter Milan 1-0 duk dai a filin San Siero din. An dakatar da wasannin kwallon kafa na kasar Italia tun lokacin da cutar Covid-19 ta barke a kasar a watan maris, Amma yanzu zasu cigana da buga wasannin nasu a wannan watan saboda sun samun saukin cutar kuma an sassauta masu dokar zaman gida. Juventus zasu buga wasan su na biyu ranar 12 ga watan yuni tsanini su da Ac Milan yayi  da su ku...