fbpx
Monday, May 23
Shadow

Tag: Coranavirus

Mutane 10 Coronavirus/COVID-19 ta kashe cikin kwana daya a Najeriya

Mutane 10 Coronavirus/COVID-19 ta kashe cikin kwana daya a Najeriya

Kiwon Lafiya
Rahotannin da hukumar kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC ta bayyana na jiya, Talata sun tabbatar da cewa mutane 10 ne suka mutu cikin awanni 24 da suka gabata sanadiyyar cutar Coronavirus/COVID-19.   Sannan rahoton ya bayyana jihar Filato a matsayin jiha mafi yawan masu kamuwa da cutar. Daga cikin jimullar mutane 239 da suka kamu da cutar a jiya, 116 daga jihar Filato suka fito. Wannan dalili yasa hankula suka koma kan jihar ta Filato. NCDC ta kuma tabbatar da mutuwar mutane 10.
Na baka kwana 21 ka bani mulki ko kuma a jimu da akai, Mataimakin gwamnan Ondo ya gayawa gwamnan da Coronavirus/COVID-19 ta kama

Na baka kwana 21 ka bani mulki ko kuma a jimu da akai, Mataimakin gwamnan Ondo ya gayawa gwamnan da Coronavirus/COVID-19 ta kama

Siyasa
Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu da cutar Coronavirus/COVID-19 ta kama kuma ya killace kansa ya ki yadda ya mikawa mataimakinsa,  Agboola Ajayi mulkin jihar, kamar yanda yake faruwa a mafi yawan jihohin da cutar ta kama gwamnan.   Mataimakin gwamnan dai a kwanakin baya mun kawo muku yanda ya bar jam'iyyar APC zuwa PDP inda har kwamishinan 'yansandan jihar ya hanashi fita da motocin gwamnati daga Ofishinsa,  lamarin da ya jawo cece-kuce. Gwamnan Akeredolu ta bakin kwamishinan Yada Labaran jihar, Donald Ojogo ya bayyana cewa ba zai mikawa mataimakin nasa ragamar jihar ba saboda ya bar gwamnati, yace har yanzu ana damawa dashi a harkar Mulki amma abinda yayi gaskiya ba za'a iya baiwa mutum irinshi ragamar mulki ba.   Saidai a nashi bangaren, Mataimakin gwamnan ya...
Coronavirus/COVID-19 ta sake bulla a kasar China

Coronavirus/COVID-19 ta sake bulla a kasar China

Uncategorized
A yayin da mutane dubu 425  suka rasa rayukansu sanadiyar annobar cutar coronavirus a duniya, a yau assabar mahukumta Pekin na kasar China, sun bayyana  rufe wasu anguwanni 11, sakamakon sake gano bulur annobar ta coronavirus a wata kasuwa dake makwabtaka da su.     A cewar mahukumtan na china, an sake samun mutane 7 da su ka kamu cutar ne a kewayen kasuwar ta Xinfadi, 6 daga cikinsu kuma an gano su ne a safiyar yau assabar. Tuni dai aka rufe makarantun faramare da kuma na reno guda 9 dake yankin.   A jimilce dai, tun ranar alhamis 11 ga watan Yuni kawo yau assabar 13 ga watan, kimanin mutane 51 aka sake gano sun kamu da cutar, 49 daga cikinsu kuma, dukkaninsu na da alaka da kasuwar ta Xinfadi ne, dake yankin kudancin birnin na Pekin. Daga cikin mutanen 49...
Rashin jin kamshi ko wari na daga cikin alamomin cutar coronavirus>>Ma’aikatar lafiya dake kasar Burtaniya

Rashin jin kamshi ko wari na daga cikin alamomin cutar coronavirus>>Ma’aikatar lafiya dake kasar Burtaniya

Kiwon Lafiya
Ma'aikatar lafiya da jin dadin jama'a dake kasar Burtaniya ta bayyana cewa rashin jin wari ko dandano na daga cikin alamomin cutar corona. Ma'aikatar ta bayyana hakan ne a ranar litinin, kamar yadda CNN ta rawaito, a  sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar ta ce daga yanzu duk wanda yaji wadannan alamomi zazzabi ko tari da rashin jin wari ko dandano ya gaggauta killace kansa daga mu'amala da mutane. A cewar rahotan ya nuna cewa mutane da dama ne a makwannin baya su ka fuskanci irin wannan matsalar na rasa jin kamshi ko wari. Hakan na zuwa ne bayan da wani kawararren masani a fannin bin diddigin alamomin cutar Tim Spector ya kalubalanci gwamnati na kin fadada bincike kan gano karin alamomin cutar. Kasar burtaniya na daga cikin jerin kasashe da suka sha fama da cutar...