fbpx
Sunday, May 22
Shadow

Tag: corona/covid19

Covid-19: An samu sabbin mutum 1,624 Da su ka kamu da cutar Coronavirus/covid-19 A Najeriya

Covid-19: An samu sabbin mutum 1,624 Da su ka kamu da cutar Coronavirus/covid-19 A Najeriya

Kiwon Lafiya
Hukumar dakile ya duwar cututtuka ta Najeriya ta fitar da sanarwar samun karin mutum 1624 a suka harbu da cutar Coronavirus a Najeriya. A sakon da hukumar ta fitar a daran jiya ya nuna cewa adadin mutum 137,654 ne a ka tabbatar da sun kamu da cutar a fadin kasar.   https://twitter.com/NCDCgov/status/1357821571394584577?s=20   Baya ga haka an sallami mutum 111,639 a kasar baki daya.
Hukumar Kula da Yara ta MDD wato Unicef ta yi gargadin cewa yaki da annobar Coronavirus na iya dalilin mutuwar kananan yara dubu shida a kowace rana

Hukumar Kula da Yara ta MDD wato Unicef ta yi gargadin cewa yaki da annobar Coronavirus na iya dalilin mutuwar kananan yara dubu shida a kowace rana

Kiwon Lafiya
Hukumar Kula da Yara ta MDD wato Unicef ta yi gargadin cewa matakan yaki da annobar Coronavirus na iya haddasa mutuwar kananan yara dubu shida a kowace rana ta Allah a kuma tsawon watanni shida a kasashe matalauta. Wani bincike da Jami'ar Johns Hopkins ta kasar Amirka ta gudanar ya nunar da cewa idan dai har mafi muni daga cikin wasu jerin hasashen guda uku da binciken ya yi ya tabbata, to kuwa kananan yara miyan daya da dubu 200 'yan kasa da shekaru biyar na iya mutuwa a cikin kasashe 118 a sakamakon yadda matakan yaki da annobar Corona za su hana kula da lafiyar yaran kamar yadda ta kamata, wannan kuwa baya ga dama wasu kananan yaran miliyan biyu da rabi da ke mutuwa a kowadanne watannin shida a wadannan kasashe matalauta.   Kazalika rahoton ya ce mata dubu 56 da 700 na iya...
Ana cin zarafin ‘yan Afirka a Chaina a sakamakon cutar corona

Ana cin zarafin ‘yan Afirka a Chaina a sakamakon cutar corona

Kiwon Lafiya
Yan kasashen Afirka kimanin dubu 15 ke zaune a birnin Guangzhou, cibiyar hada-hadar kasuwanci a kasar Chaina. A farkon watan Afrilu an kore su daga gidajen haya, an kuma killace su a dole da sunan yaki da cutar corona.   Ko da yake yanzu abubuwa sun lafa a birnin na Guangzhou kuma mahukuntan Chaina sun amsa cewa sun tabka kurakurai, amma matakan da ake dauka dangane da corona sun nuna a fili yadda ake fama da matsalar wariyar launin fata a Chaina. A wata ma'aikatar sarrafa tufafi da ke Guangzhou din, an hana baki ma'aikata shiga ciki. Ga tunani da yawa na al'ummar Guangzhou, baki musamman bakaken fata na da babbar kasadar yada kwayar cutar coronavirus fiye da 'yan Chaina.
Coronavirus ta kashe Amurkawa sama da dubu 3 a kwana daya

Coronavirus ta kashe Amurkawa sama da dubu 3 a kwana daya

Uncategorized
Sama da mutane miliyan 2 da dubu 675 suka kamu da kwayar cutar a kasashen duniya 193, inda fiye da dubu 700 suka warke. Kasar Amurka kadai, cutar ta kashe kusan mutane dubu 50, da suka hada da dubu 3 da 176 da ta kashe cikin sa'o'i 24 da suka gabata. Amruka ce ke sahun gaba wajen samun asarar rayuka, italiya ce ke matsayi na biyu da asarar mutane dubu 25 da 549 , sai kuma dubu 23 da 157 da suka mutu a Spain, yayin da a Fransa, adadin mamatan ya kai dubu 21 da 856, sai kasar Birtaniya da ta yi asarar mutane dubu 18 da 738 a sanadiyar annobar ta coronavirus.
Coronavirus ta lakume rayukan mutane kusan dubu 130 a fadin duniya

Coronavirus ta lakume rayukan mutane kusan dubu 130 a fadin duniya

Kiwon Lafiya
Coronavirus ta kashe mutane kusan dubu 130 a fadin duniya A yanzu alkaluma sun nuna cewa cutar corona ta kama adadin kusan mutum miliyan 2 wadanda suka mutum sun Kai kimanin mutum dubu 127,898 a sakamakon annobar. A kasar Amurka an samu asarar rayukan mutane dubu 26 da 59 wanda mutane sama da dubu 600 da sun harbu da cutar. A Italiya kuwa, coronavirus ta kashe mutane dubu 21 da 69, sai Spain mai mutane dubu 18 da 579, a Faransa kuwa, mutane dubu 15 da 729 suka mutu, yayin da a Birtaniya aka samu asarar rayukan mutane kusan dubu 13. Wanda a yanzu kasar Amurka ke akan gaba da adadin mutum dubu 26 da 59.
An tantance mutum 46 a jihar kano bisa zargin suna dauke da cutar Corona

An tantance mutum 46 a jihar kano bisa zargin suna dauke da cutar Corona

Kiwon Lafiya
An tantance mutum 46 a jihar kano bisa zargin suna dauke da cutar Corona Ma'aikatar lafiya ta jihar Kano tace sakamakon gwajin cutar Corona da a kaiwa mutum 46 ya nuna ba sa dauke da cutar, inda a yanzu haka ake jiran sakamakon mutum 4. Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Muhammad Ibrahim tsanyawa ne ya bayyana haka. Ya bayyana cewa har yanzu jihar Kano bata da mutum guda mai dauke da cutar. Tsanyawa ya Kara da cewa ma'aikatar lafiya ta jihar Kano ta shirya tare da yin tsare tsare domin dakile ya duwar cutar inda ya kara da cewa hakan ne yasa gwamnati taga da cewar karawa ma'aikata hutu har na makwanni 2.
Covid-19: Yan Najeriya basu san bala’in coronvirus ba

Covid-19: Yan Najeriya basu san bala’in coronvirus ba

Uncategorized
Covid-19: 'Za a kai lokacin da mutane za su soma faduwa suna mutuwa a Najeriya' Masana harkar lafiya a Najeriya sun fara nuna damuwa kan yadda jama'a ke daukar batun coronavirus, inda suke kunnen kashi da shawarwarin da jami'an lafiya ke bayarwa. Farfesa Usman Yusuf wanda shi ne tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta Najeriya ya ce abin da suke gani yana tayar wa da duk wani masanin harkokin lafiya hankali. Farfesa Usman ya shaida wa BBC cewa idan jama'a ba su sauya yadda suke daukar cutar ba, to za ta iya yin mummunar illa. Ya ce hankalin likitoci a Najeriya da na kasashen ketare a tashe yake, domin sun ga yadda ta fara a China, inda dimbin jama'a suka rasa rayukansu daga nan ta bazu kasashen duniya. "Ta zo Italiya da Spain yanzu tana Ingila har da shugabansu, Firai m...
COVID-19: Afurka ba dakin gwaje-gwaje bane dan wasan kasar ivory coast Didier drogba ya mayar da martani ga likitocin da suka bada shawara a gwada maganin cutar covid-19 a kan yan afurka

COVID-19: Afurka ba dakin gwaje-gwaje bane dan wasan kasar ivory coast Didier drogba ya mayar da martani ga likitocin da suka bada shawara a gwada maganin cutar covid-19 a kan yan afurka

Kiwon Lafiya
An tafka mahawara inda aka zargi likitocin Faransa biyu da wariyar launin fata saboda ba da shawarar cewa, ya kamata a fara yin gwajin rigakafin cutar coronavirus a kan mutane a Afirka. An yi wannan tsokaci ne ta tashar talabijin ta Faransa, LCI, yayin wata tattaunawa a ranar Laraba game da jarabawa akan COVID-19 da za a gabatar a Turai da Ostiraliya don ganin ko za a iya amfani da maganin na BCG don magance cutar. Shima dai tsohon Dan wasan kasar Ivory Coast Didier Drogba wanda ya taka leda a kungiyar kwallan kafa ta Chelsea ya rubuta a shafin shi na sada zumunci inda yayi Allah wa dai da magan ganun likitocin ya kirashe da wariyar launin fata ne ya kuma kira da cewa Afirka ba dakin gwaje gwaje bane. A cewar Olivier Faure, na Jam'iyyar Gurguzu ta Faransa, ya ce kalaman likitoci...
Nan bada jimawa ba gungun likitoci daga kasar Chana za su iso Najeriya domin tallafawa kasar wajan yaki da cutar Covid-19

Nan bada jimawa ba gungun likitoci daga kasar Chana za su iso Najeriya domin tallafawa kasar wajan yaki da cutar Covid-19

Kiwon Lafiya
Bayan nasarar da kasar chaina ke samu wajan yaki da cutar Covid-19 ya zuwa yanzu kasar ke ta kokari wajan magance matsalar a fadin duniya baki daya ta hanyar taimakawa wasu kasashe dan dakile ya duwar cuta gaba daya. Da alamu kasar najeriya ita ma tabi sahun samun wannan taimako idan mukai duba da bayanin ministan lafiya, inda Gwamnatin tarayyar ta ce wani gungun Kwararrun likitoci 18 da suka hada da likitoci da ma'aikatan jinya daga kasar Chaina za su isa Najeriya nan da yan kwanaki. Ministan Lafiya, Osagie Ehanire ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a taron tattaunawa na yau da kullum na kwamitin shugaban kasa kan COVID-19 a Abuja ranar Juma’a. Ehanire ya kuma ce, wasu kamfanonin kasar Sin da ke aiki a Najeriya, su ma sun bayar da tallafin su don tai makawa Najeriya a...