
Amitabh Bachchan ya ƙaryata labarin cewa ya warke daga korona
Shahararren ɗan wasan fim ɗin Indiya Amitabh Bachchan ya musanta wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta da wasu na talabijin da ke cewa ya warke daga cutar korona.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Amitabh ya ce labarin da ake wallafawa kansa na ƙarya ne.
A ranar Asabar 11 ga watan Yuli ne aka kwantar da Amitabh Bachchan asibiti sakamakon cutar korona.
An kuma kwantar da wasu daga cikin makusantansa a asibiti sakamakon su ma sun kamu da cutar