fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Tag: Coronavirus/COVID-19 Kano

COVID-19: Yawan majinyata zai karu a Kano>>Ganduje

COVID-19: Yawan majinyata zai karu a Kano>>Ganduje

Uncategorized
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano ya ce akwai yiwuwar adadin wadanda suka kamu da coronavirus ya karu matuka saboda kafa sabbin cibiyoyin gwajin cutar a jihar.     Ganduje ya fadi haka ne yayin wani taron manema labarai da Kwamitin Kar-ta-Kwana a kan Yaki da COVID-19 ya kira ranar Juma’a a Gidan Gwamnati da ke Kano.     Ya kuma ce tuni aka kammala shirye-shiryen kakkafa wasu cibiyoyin gwajin a kananan hukumomi 36 masu nisa daga babban birnin jihar.   “Wajibi ne mu kafa karin cibiyoyin gwaji a kananan hukumomi 36 masu nisa.     “Za mu ci gaba da shiri don gaba, akwai bukatar da an ce kule mu ce cas.     “Za mu tabbatar da cewa an kafa dukkan cibiyoyin da suka dace don kada a mana sakiyar da ba ruw...
Coronavirus ta janyo cacar-baki tsakanin Ganduje da El-Rufai

Coronavirus ta janyo cacar-baki tsakanin Ganduje da El-Rufai

Siyasa
Da alama sakonnin da gwamnan jihar Kadunan Najeriya Malam Nasir El-Rufai, ya rinka wallafawa a shafinsa na Twitter a baya-bayan nan kan almajiran da aka mayar da su jihar daga Kano sun bata wa Ganduje rai.     A makon jiya Gwamna El-Rufai ya wallafa wani sakon Twitter inda ya ce galibin masu dauke da cutar korona a jihar almajirai ne da gwamnatin Kano ta koma da su Kaduna.     Hasalima a sakon da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar 4 ga watan Mayu, ya ce a cikin mutum 72 da suka kamu da cutar a ranar, "kashi 65 almajirai ne da aka dawo da su daga jihar Kano."   Sai dai gwamnatin Kano ta ce ba da gangan take mayar da almajiran jihohinsu na asali ba.     Wata sanarwa da Malam Abba Anwar, mai magana da yawun Gwamna...
Ma’aikatan lafiya 47 ne suka kamu da cutar korona a Kano

Ma’aikatan lafiya 47 ne suka kamu da cutar korona a Kano

Uncategorized
Akalla ma'aikatan lafiya 47 ne a Kano suka kamu da cutar korona kamar yadda gwamnatin jihar ta sanar. Babban jami'i a kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin yaki da cutar korona, Dr Tijjani Hussain ne ya tabbatar da hakan yayin wani jawabi ga manema labarai ranar Lahadi. Dr Tijjani ya ce an tabbatar da kamuwar ma'aikatan lafiyar da cutar ne a 'yan makonni da suka gabata, inda ya ce ba a samu karin wani ma'aikacin lafiyar da ya sake kamuwa ba. Jihar Kano ce dai jiha ta biyu a jerin jihohin da ke da yawan adadin masu dauke da cutar korona a Najeriya. Adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar korona a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun kai 602, a cewar ma'aikatar lafiya ta jihar.