
Yawan Masu Coronavirus/covid-19 ya zarta Miliyan 20 a Fadin Duniya
Rahotanni sun bayyana cewa, yawan masu cutar Korona a fadin Duniya sun zarta Milliyan 20.
A daran Ranar Lahadin data gabata adadin yawan masu fama da cutar ya karu, inda yawan masu cutar ya kai kimanin 20,016,286, yayin da kimanin mutane 733,592 suka mutu sakamakon cutar coronavirus a fadin Duniya.
Ya zuwa yanzu kasashe guda Uku ne, cutar tafi ta'azzara, wadanda suka hada da kasar Amurka, Brazil sai Kasar India.