fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: Coronavirus/COVID-19 Saudiyya

Da Dumi-Dumi:A ranar Lahadi me zuwa Saudiya zata bude Masallacin Ka’aba bayan watanni 3 a kulle

Da Dumi-Dumi:A ranar Lahadi me zuwa Saudiya zata bude Masallacin Ka’aba bayan watanni 3 a kulle

Siyasa
Kasar Saudiyya ta bayyana cewa a ranar Lahadin karshen makonnan da muke ciki ne idan Allah ya kaimu zata bude masallacin Ka'aba bayan shafe watanni kusan 3 a kulle kamar yanda kafafen watsa labaran kasar suka sanar.   An rufe masallacin Ka'abane dan dakile yaduwar cutar. Saidai uk da matakan da kasar ta dauka na dakile cutar, ana samun karuwar masu kamuwa da ita.   Ma'aikatar kula da addini ta kasarce ta fitar da sanarwar bude Ka'aba, kamar yanda gidan talabijin din kasar, Al-Ekhbariya ya ruwaito ta hanyar kamfanin dillancin labarai na AFP.   Guraren tarihi na Makkah zasu dawo ci gaba da Karbar Baki, kamar yanda sanarwar ta bayyana saidai sanarwar bata bayyana ko za'a yi aikin hajjin bana ba ko a'a.   Masu Coronavirus/COVID-19 150,000 kasar Saudi...
Saudiyya za ta yanke shawara kan makomar hajjin 2020

Saudiyya za ta yanke shawara kan makomar hajjin 2020

Siyasa
Ministan harakokin lamurran addini da kuma haɗin kan addinai na Saudiyya Sahibzada Noor-ul-Haq Qadri ya ce a ranar Litinin ne 15 ga watan Yuni gwamnatin ƙasar za ta yanke shawara ta ƙarshe game da makomar Hajjin 2020. Da yake bayani a wani taron tuntuba a ranar Alhamis, ministan ya ce gwamnatin Saudiyya za ta ɗauki matakin da ya fi dacewa saboda maniyyata aikin Hajji, sannan gwamnatin ta daɗe tana nazari tare da duba hanyoyi da dama game da aikin Hajjin. Ya ce ana ci gaba da maharawa game da yadda za a tafiyar da aikin Hajjin a ma’aikatarsa, yana mai cewa Hajjin ba za ta kasance kamar yadda aka saba ba domin za a rungumi matakai na kaucewa yaɗuwar cutar korona. Ma’aikatar lamurran addinin ta Saudiyya ta kuma ce ta bayar da umurni bincike kan ƙiyasin kuɗaɗen aikin hajji, idan har S...
Gobe Lahadi za a buɗe Masallacin Madinah

Gobe Lahadi za a buɗe Masallacin Madinah

Siyasa
Gwamnatin Saudiyya ta bayar da umarnin buɗe masallacin Manzon (SAW) da ke a garin Madinah a gobe Lahadi. Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa tuni hukumar da ke kula da manyan masallatan ƙasar biyu ta gama shirye-shiryen buɗe masallacin tare da sharuɗɗa masu tsauri. An bayyana cewa kashi 40 cikin 100 na yawan mutanen da masallacin zai iya ɗauka kaɗai za a iya bari su yi sallah a lokaci guda.
Kasar Saudiyya ta dakatar da kudin tallafin da take baiwa ‘yan kasar ta, ta kuma kara kudin haraji ninki 3

Kasar Saudiyya ta dakatar da kudin tallafin da take baiwa ‘yan kasar ta, ta kuma kara kudin haraji ninki 3

Siyasa
Kasar Saudiyya ta sanar da dakatar da baiwa 'yan kasarta tallafin kudin da take basu saboda rage musu radadin tsadar farashin kayayyaki a kasar sanna kuma ta kara kudin harajin VAT da ninki 3.   Saudiyya ta dauki wannan matakine saboda faduwar farashin gangar danyen mai a kasuwannin Duniya mafi muni sandin rashin sayen man dalilin zuwan Annobar cutar Coronavirus/COVID-19.   Ministan kudi na kasar, Muhammad Al-Jadaan ya bayyana haka inda yace sun tsayar da bayar da kudin tallafin da kuma kara harajin VAT daga kashi 5 zuwa kashi 15, kamar yanda kamfanin dillancin labaran kasar ya ruwaito.   Kasar Saudiyya, wadda itace ta daya wajan fitar da mai a Duniya kuma da shi ta dogara wajan samun kudin shiga na kashe Biliyoyin kudi wajan baiwa 'yan kasar tallafin r...
Coronavirus: Kasar Saudiyya ta samar da kofa mewa mutane feshin Magani kamin su shiga Masallacin Ka’aba

Coronavirus: Kasar Saudiyya ta samar da kofa mewa mutane feshin Magani kamin su shiga Masallacin Ka’aba

Uncategorized
Kasar Saudiyya ta samar da wata kofa mewa mutane feshin abin tsaftace jiki kamin kamin shu shiga Masallacin Ka'aba,  kamar yanda kamfanin dillancin Labaran kasar, SPA ya ruwaito. Kofar da mutum ya zo wucewa da kanta zata fesheshi da abin tsaftace jiki. https://www.youtube.com/watch?v=UW1BR6WEB6Y A baya dai kasar ta Saudiyya ta saka wasu kyamarori na musamman a masallatan Ka'aba dana Annabi (SAW) wanda sukan gane yanayin zafin jikin mutum.   A lokaci 1 Kyamarorin na gano yanayin zafin jikin mutane 25, duk wannan kokarine na ganin an dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19.
Masana a Italiya sun bayyana cewa sun samo Rigakafin Coronavirus/COVID-19 na farko a Duniya

Masana a Italiya sun bayyana cewa sun samo Rigakafin Coronavirus/COVID-19 na farko a Duniya

Uncategorized
Wasu masana a kasar Italiya dake birnin Rome sun bayyana cewa sun samo rigakafin cutar Coronavirus/COVID-19.   Daily Mail ta ruwaito cewa masanan sun ce tuni suka gwada Rigakafin akan bera kuma yayi aiki inda yanzu suna shirin gwadashine akan mutum.   Daya daga cikin wanda suka yi aikin samar da Rigakafin ya bayyana cewa a iya saninsa sune na farko a Duniya suka samar da rigakafin cutar.   Jami'ar Oxford na daga cikin wanda ke neman rigakafin cutar inda suke shirin samar dashi a watan Satumba na shekarar nan.   Wani me kula da bangaren lafiya na jami'ar Matt Hancock ya bayyana cewa da wuya a samu maganin cutar saidai a samar mata da riga kafi.
Saudiyya ta sassauta dokar zaman gida Dole saidai dokar zata ci gaba da aiki a garin Makka

Saudiyya ta sassauta dokar zaman gida Dole saidai dokar zata ci gaba da aiki a garin Makka

Uncategorized
Kasar Saudiyya ta sassauta wasu daga cikin matakan hana zirga-zirga da ta saka a ranar Lahadi. Dokar hana fita ta ba-dare-ba-rana da aka saka, an dage ta daga karfe 9:00 na safe zuwa 5:00 agogon kasar. Daga ranar Laraba kuma shaguna za su samu damar budewa sannan wasu ma'aikatun su dawo bakin aiki. Sassaucin wanda zai kai har mako biyu na watan watan Ramadana, bai hada da wuraren da za a samu taruwar jama'a ba kamar wuraren cin abinci da na yin atasaye. Biranen Makkah da Madinah za su ci gaba da kasancewa cikin dokar hana zirga-zirga. Fiye da mutum 16,000 ne aka tabbatar sun kamu da cutar korona a kasar sannan wasu 136 suka mutu. Dokar ta bukaci a rika tsaftace shagunan siyayya a kowane awanni 24 da kuma hana yara kasa da shekaru 1t shuga shagunan sannan ba'a ...
Coronavirus/COVID-19 ta sake kashe wani mutun a Kano

Coronavirus/COVID-19 ta sake kashe wani mutun a Kano

Kiwon Lafiya
Rahotanni daga jihar Kano na cewa ana zargin cutar Coronavirus/COVID-19 ta kashe Regional Manaja me kula da yankin Kano na bankin First Bank, Abdullahi Lawal.   Rahotanni daga iyalan mamacin sun bayyana cewa, ya fara rashin lafiyane sai aka garzaya dashi wani asibiti me zaman kansa a Kano.   Daga nanne sai aka turasu zuwa Asibitin Aminu Kano, Marigayin dai ya rika tari da zazzabi da kuma numfashi sama-sama kamin daga baya ya rasu.   Wata Hajiya Salma Ahmad wadda ta bayyana kanta a matsayin surukar Mamacin,kamar yanda independent ta ruwaito an jiyota tana magana a wata murya da aka nada data watsu sosai.   Matar ta rika zargin hukumar NCDC ta Kano da kin kawo musu dauki cikin gaggawa inda akai ta kiran wayarsu amma suka ki dauka.   ...
COVID-19: A kwai yiwuwar gudanar da aikin hajjin bana

COVID-19: A kwai yiwuwar gudanar da aikin hajjin bana

Kiwon Lafiya
Ana sa ran yiwuwar gudanar da aikin hajjin bana Duk da cewa har yanzu duniya ba ta warke daga annobar coronavirus ba amma a cewar Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta ce, ta samu bayanai daga Saudiya na nuna cewa, akwai yiwuwar gudanar da aikin hajjin bana. A cewar shugaban hukumar al'hazai ta Najeriya Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ne ya bayyana cewa ma'aikatar kiwan lafiya dake kasar Saudiya tai harsashan cewa watakila a iya fara samun raguwar ya duwar cutar Corona a nan da 21 ga watan afrilu da muke ciki, kafun ai nasarar kawar da cutar anan da watan mayu. injishi Hakanne ya baiwa hukumar aikin hajji ta kasa kwarin gwaiwar ci gaba da shirye-shiryan ta kamar yadda ta sanar.
An yi wa Sule Lamido gwajin coronavirus

An yi wa Sule Lamido gwajin coronavirus

Kiwon Lafiya
Tsohon gwamnan jihar Jigawa da ke Najeriya, Alhaji Sule Lamido, ya ce an yi masa gwajin covid-19, cutar sarkewar numfashi da coronavirus ke haddasawa. A sakon da ya wallafa a shaifinsa na Facebook ranar Litinin, tsohon gwamnan ya ce daraktan kiwon lafiya na ma'aikatar lafiyar jihar Kano, Dr Imam Wada Bello ne ya aika masa da sakon da ke neman ya mika kansa a yi masa gwaji saboda ya halarci jana'iza ranar Alhamis wacce shi ma mutumin nan da aka gano yana dauke da cutar a Kano ya halarta. "Muna so ka ba mu dama mu gwada ka domin ganin ko akwai yiwuwar kana cikin hatsarin kamuwa da cutar", in ji sakon. Gwamnan ya ce da misalin karfe daya da rabi na ranar Litinin shi da direbansa da jami'in tsaron da ke ba shi kariya aka yi musu gwajin coronavirus. Ya ce suna jiran sakamako...