Monday, March 30
Shadow

Tag: Coronavirus/COVID-19

Neymar ya musanta cewa be killace kansa kan Coronavirus/COVID-19 ba

Neymar ya musanta cewa be killace kansa kan Coronavirus/COVID-19 ba

Wasanni
Neymar ya karyata cewa shi bai karya dokar da aka sa ta yin nesa da mutane ba daya koma kasar shi ta Brazil alhalin ya saka hotunan shi a shafin shi na Instagram tare da abokan shi suna buga wasan raga (volley ball). Dan wasan mai shekaru 28 yace mutanen da yayi hotunan da su dama tare suka tafi daga Paris a jirgi izuwa kasar Brazil kuma suna killace kansu tare da shi ne.Kuma ya Kara da cewa yana cigaba da motsa jikin ne kamar yadda ya saba. Mai magana da yawun Neymar yace: Neymar ya gayyaci wa'yanan mutanen ne don su killace kansu na tsawon kwanaki 14 kafin su tafi wajen iyalan su. Kuma ya Kara da cewa yaron shi Davi luka ne kadai ya ziyarce shi ayayin da yake killace kanshi amma ya guji sauran iyalan shi harda mahaifiyar shi da yar uwar shi da kakar shi.
Bidiyo: Yanda Gwamna Kano ya hana wata mota cike da ‘yan cirani shiga Kano

Bidiyo: Yanda Gwamna Kano ya hana wata mota cike da ‘yan cirani shiga Kano

Kiwon Lafiya
A makon daya gabatane gwamnatin jihar Kano ta sa dokar hana shiga da fita cikin jihar a kokarin da take na dakile shigar cutar Coronavirus/COVID-19 cikin ta.   Gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a yau ya fita rangadi dan ganin yanda wannan doka take aiki.   Yaci karo da wata motar daukar kaya wadda take dauke da mutane a cikinta inda nan take yasa aka kaita ofishin 'yansanda dan daukar matakin daya kamata.   https://twitter.com/dawisu/status/1244656304301498368?s=19 Hadimin gwamnan Kanon kan sadarwa, Salihu Tanko Yakasai ne ya bayyana haka ta shafinsa na sada zumunta.   Gwamnan ya kirawo direban motar ya sauko kasa inda ya tambayeshi shin daga ina ya dauko wadannan mutanen? https://twitter.com/dawisu/status/1244656827373060096?s=19 ...
Lafiyata Qalau>>Inji Matar da gwamnan Jihar Benue yace ta kamu da cutar Coronavirus/COVID-19

Lafiyata Qalau>>Inji Matar da gwamnan Jihar Benue yace ta kamu da cutar Coronavirus/COVID-19

Kiwon Lafiya
Wata mata a jihar Benue da aka bayyanata cewa tana dauke da cutar Coronavirus/COVID-19 ta karyata inda tace bata dauke da cutar.   Matar me suna Susan Okpe me shekaru 54 ta bayyana cewa kawai ta ji Gwamnan jihar, Samuel Ortom yana gayawa Duniya cewa ta kamu da cutar Coronavirus/COVID-19 Alhali ita bata san da wannan zancen ba.   Ta kara da cewa ita dai tasan cewa an dauki samfurin jininta za'a yi gwaji amma bata ga sakamakon gwajin nata ba.   Matar wadda ta zo Najeriya daga kasar Ingila inda acan take da zama ta bayyanawa Sahara Reporters cewa kamin ta taso daga Ingila an mata gwaji kuma ya nuna cewa bata da cutar.   Ta kara da cewa zuwanta Najeriya saboda gajiyar tafiya yasa ta fara masassara hakan ne yasa aka fara mata kulawar Malaria. Tace tan...
Jahilci ne malami ya karyata coronavirus>>JNI

Jahilci ne malami ya karyata coronavirus>>JNI

Kiwon Lafiya
Kungiyar Musulman Najeriya ta Jama'atu Nasril Islam JNI karkashin jagorancin Sarkin Musulmai ta ce jahilci ne wani malamin addini ya fito yana ikirarin cewa coronavirus karya ce.     Kungiyar ta fitar da sanarwa ne ranar Litinin mai dauke da jan kunne ga malaman da sanarwar ta ce suna dulmuyar da al'umma kan cutar Covid-19 a Najeriya.     Sanarwar dai martani ce ga wasu rukunin malaman addinin Islama da suka fito suna wa'azi ga mabiyansu suna karyata cewa coronavirus karya ce makirci ne, cikinsu har da wasu manyan malaman da ke da'awa.     A cikin sanarwar da sakataren kungiyar JNI ya fitar Dr. Khalid Abubakar Aliyu, ya ce bai kamata irin wadannan kalamai su fito bakin duk wani malami ba da ya amsa sunansa malam.   Kungiyar ...
Yarima mai jiran gado ya samu yanci bayan ya kange kansa a sakamakon kamuwa da cutar Covid-19

Yarima mai jiran gado ya samu yanci bayan ya kange kansa a sakamakon kamuwa da cutar Covid-19

Kiwon Lafiya
Yarima Charles ya fita daga kange kansa da yayi. Tun bayan gwajin cutar Coronavirus da akai wa mai jiran kujerar sarauniyar ingila a yau ya samu yanci cewar mai magana da yawun sa. Charles mai shekaru 71 da haihuwa shine yarima mai jiran gado. Mai magana da yawun nasa ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa inda yace bisa ga shawar-warin likitansa yarima ya fita daga kange kansa, inda a yanzu ya ke murmurewa bayan rahotan da ya nuna ya kamu da cutar covid-19.
Fiye da mutum 723,000 sun kamu da coronavirus

Fiye da mutum 723,000 sun kamu da coronavirus

Kiwon Lafiya
Alkaluman da cibiyoyin da ke bibiyar yaduwar coronavirus suka fitar ranar Litinin da safe sun nuna cewa fiye da mutum 723,740 ne suka kamu da cutar a fadin duniya. Jami'ar Johns Hopkin, wacce ke bayar da bayani kai-tsaye game da halin da ake ciki a kan cutar, ta kara da cewa mutum 34,018 ne suka mutu, yayin da mutum 152,042 suka warke daga coronavirus ya zuwa safiyar ta Litinin. Ga kasashe goman farko da suka fi kamuwa da cutar: Amurka - 143,025 Italiya - 97,689 China - 82,152 Spain - 80,110 Jamus- 62,435 Faransa - 40,723 Iran - 38,309 Birtaniya - 19,784 Switzerland - 14,829 Netherlands - 10,930 BBChausa.
Cikin hadiman sanatoci 10 da suka killace kansu saboda Coronavirus/COVID-19 ya duri ruwa

Cikin hadiman sanatoci 10 da suka killace kansu saboda Coronavirus/COVID-19 ya duri ruwa

Kiwon Lafiya
Akwai sanatocin Najeriya 10 da ana tsaka da Annobar Coronavirus/COVID-19 suka je kasar Ingila inda suka halarci wani zaman majalisa na musamman   Bayan dawowarsu gida, Sanatocin sun ci gaba da mu'amalarsu harma sun shiga majalisar.   Saidai ya zuwa yanzu ba'asan ko suna dauke da cutar ba ko kuwa a'a, lamarin sanatocin da suka ki kai kansu a gwadasu duk da cewa sun dawone daga kasar waje kamar yanda doka ta tanada ya dauki hankula sosai.   Hakanan sanatocin basu killace kansu na tsawon kwanaki 14 kamar yanda doka ta tanada ba, in banda sanata 1 a cikinsu, Ajibola Basiru da ya bayyana cewa shi ya killace kansa.   Me magana da yawun majalisar,Sanata Godiya Akwashiki ya bayyana cewa dalilin kulle majalisar na tsawon makonni 2 shine duka 'yan majalisa...
Abubuwan Da Shugaba Buhari Ya Fada a Jawabinsa Kan Coronavirus

Abubuwan Da Shugaba Buhari Ya Fada a Jawabinsa Kan Coronavirus

Kiwon Lafiya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi da yammacin jiya, inda ya bayar da umurnin dakatar da zirga-zirga na tsawon mako biyu a Abuja, Legas da kuma Ogun don rigakafin cutar Coronavirus.   Wannan umarnin dai zai fara aiki ne daga ranar 30 ga watan maris, da karfe 11 na dare.   Shugaban ya jaddada cewa dukkannin mutanen da ke zaune a wadannan wuraren, ya zama tilas su zauna a gida kuma a dakatar da tafiya zuwa ko kuma dawowa daga biranen.   A jawabin nasa, shugaban ya ce gwamnatinsa za ta tura tallafi ga jama’ar da ke kewayen manyan biranen da rashin fitowar zai shafa.   Duk da haka shugaban ya ce masu gudanar da muhimman ayyuka irin jami’an tsaro, masu aikin lantarki, man fetur, raba a
Gwamnatin Nijar ta daukewa talakawa biyan kudin wuta da ruwa

Gwamnatin Nijar ta daukewa talakawa biyan kudin wuta da ruwa

Kiwon Lafiya
Shugaban Jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou, ya sanar da wasu sabbin matakai don yaki da cutar Coronavirus a kasar, matakan da suka fara aiki daga ranar 28 ga wannan wata na Maris.   Wasu daga cikin matakan da gwamnatin Nijar din ta dauka kan annobar sun hada da hana fita daga karfe 7 na yamma zuwa 6 na safe a birnin Yamai inda a can ne cutar ta fi tsananta, tare da hana shiga ko fita daga birnin tsawon makwanni biyu daga ranar 28 ga wannan wata na Maris.   Shugaba Issoufou ya kuma bada umarnin soma farautar wadanda ake zaton cewa suna dauke da kwayar cutar a duk inda suke, domin yi masu gwaji a cibiyoyin kiwon lafiya da ke da kwarewa dangane da cutar.   Domin samar wa jama’a sauki wajen samun kayayyakin da ake amfani da su wajen tsafta da kuma kashe kwaya