
Ana tsaka da Coronavirus/COVID-19, Kasar Costa Rica ta halasta Auren Jinsi
Kasar Costa Rica dake yankin Nahiyar Amurka ta tsakiya ta halasta auren jinsi a daren jiya.
Babu wani shagali da aka yi kamar yanda aka saba yi a kasashen dake Halasta wannan aure saboda Annobar cutar Coronavirus/COVID-19 amma dai an watsa shirye-shiryen da suka danganci auren jinsi a gidajen talabijin na kasar.
Hakanan nan da nan aka samu auren jinsi na farko a kasar.
Shugaban kasar Carlos Alvarado ya bayyana cewa wannan shirine na musaman da zai canja al'ada da yanyin zamantakewa a kasar inda yace hakan zai baiwa mutane da dama yin aure.
Shugaban kasar dai ya samu nasara a zaben da akayi a kasar saboda goyon bayan da yake baiwa auren jinsi inda ya kayar da me ra'ayin addinin Kiristanci, Fabricio Alvarado.