fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: covid/19

Yan daba sun fasa rumbun ajiyar kayan tallafin COVID-19 a Ondo, inda suka yi awon gaba da kayan, sannan suka cinna ma Rumbun wuta

Yan daba sun fasa rumbun ajiyar kayan tallafin COVID-19 a Ondo, inda suka yi awon gaba da kayan, sannan suka cinna ma Rumbun wuta

Siyasa
Yan daba sun fasa cikin rumbunan ajiyar gwamnati a Akure, babban birnin jihar Ondo, kuma sun wawushe kayayyakin tallafi na COVID-19 da aka ajiye a can. A cewar rahotanni daga baya suka kone gidan ajiyar. Gidan ajiyar yana cikin harabar babban kotun majistare a cikin garin Akure. Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Gwamnatin Tarayya ce ta baiwa jihar tallafin. Gwamna Rotimi Akeredolu yayi bikin kaddamar da kayan tallafi na CA-COVID 19 a Akure, babban birnin jihar a ranar 10 ga watan Agustan wannan shekarar. Bayan samun bayanan sirri, an gano cewa 'yan daban sun afka cikin dakin ajiyar kayan ne suka fasa kofofin, suka yi awon gaba da kayan. Sai da sojoji suka shiga tsakani don kawo karshen lamarin a Akure, babban birnin jihar Ondo. Wani faifan bidiyo da ya nuna ...
An samu sabbin mutum 790 wanda suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya Jimulla 26,484

An samu sabbin mutum 790 wanda suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya Jimulla 26,484

Kiwon Lafiya
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka NCDC ta sake fidda sanarwar kara samun adadin mutum 790 wanda suka harbu da cutar coronavirus a fadin kasar. Sanarwar wanda hukumar ta wallafa ta cikin shafinta dake kafar sadarwa a ranar laraba 1 ga watan Yuli na shekara ta 2020. Haka zalika hukumar ta zayyana jahohin da aka samu karin masu cutar wadanada suka hada da: Delta-166 Lagos-120 Enugu-66 FCT-65 Edo-60 Ogun-43 Kano-41 Kaduna-39 Ondo-33 Rivers-32 Bayelsa-29 Katsina-21 Imo-20 Kwara-18 Oyo-11 Abia-10 Benue-6 Gombe-4 Yobe-2 Bauchi-2 Kebbi-2. Bayan haka cibiyar ta bada rahoton sallamar adadin mutum 10,152 sannan kuma an samu.mutuwar mutum 603 a fadin kasar.
COVID-19: Gwamnatin Kano zata fara raban tallafin kayan abinci

COVID-19: Gwamnatin Kano zata fara raban tallafin kayan abinci

Siyasa
Raban kayan tallafi ga al'ummar jihar Kano karkashin gwamna ganduje domin rage radadi ga al'ummar jihar. Kwamitin tallafin da gwamnatin jihar Kano ta kafa na neman taimako kan bullar cutar corona ya bayyana cewa tuni tsare-tsare sunyi nisa, domin ganin an fara gudanar da rarraba kayayyakin abinci da aka tara domin tallafawa al'ummar Jihar kano, domin rage musu radadin halin da suke ciki game da cutar Covid-19. Farfesa Muhammad Yahuza Bello shugaban jami'ar Bayaro dake kano wanda kuma shine shugaban kwamitin tallafin wanda ya bayyana hakan ga yan jarida a yayin wata tattauna da akai dashi. Farfesa Bello ya kuma bayyana cewa an samu nau'in kayan abinci kimanin buhu dubu uku, da dari uku hadi da tallafin kudi da ya kai Naira miliyan dari uku da saba'in da shida, gami da shauran k...
Sakamakon gwajin matar Gwamnan kaduna ya fito

Sakamakon gwajin matar Gwamnan kaduna ya fito

Kiwon Lafiya
Uwar gidan gwamnan Kaduna Malam Nasiru El Rufa'i Hajiya Hadiza Isma El-Rufai, biyo bayan gwajin da akai mata a ranar lahadi a yau sakamakon nata ya fito inda sakamakon nata ya nuna cewa bata kamu da cutar Covid-19 ba. Tun bayan sanarwar da mai gidan ta ya bayar cewa ya kamu da cutar Coronaviru a ranar asabar, biyo bayan haka sai Uwar gidan nasa itama aka tabbatar da yi mata gwaji domin duba lafiyarta wanda daga bisani ne rahoto ya bayyana bata dauke da cutar. A ranar litinin ne uwar gidan gwamnan ta bayyana a shafinta na sada zumunci cewa sakamakon gwajin da akai Mata ya nuna bata dauke da cutar. Bayan bayyanar hakan itama cibiyar kula da cututtuka ta kasa ta bayyana Kara samun sabbin wanda suka kamu da cutar har kusan mutum 20 wanad biyu daga cikin su yan jihar kaduna ne.
Wani matashi dan Najeriya yarasa ransa a sakamakon kamuwa da cutar Covid-19 a kasar Amurka

Wani matashi dan Najeriya yarasa ransa a sakamakon kamuwa da cutar Covid-19 a kasar Amurka

Kiwon Lafiya
Yadda wani matashi dan Najeriya ya mutu a sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus a kasar Amurka. Matashin dai mai shekaru 25 mai suna Bassey Offiong dalubi ne wanda yake karanta chemical engineering a kasar Amurka wanda ya rage befi sati ya kammala karatunsa na digiri ba, kamar yadda jaridar Detroit News suka rawaito. A cewar yar uwar mamacin Asari Offiong ta bayyana cewa dan uwanta ya fada mata cewa yana jin numfashin shi yana daddaukewa sannan ga zazzabi mai zafi, wanda duka alamomine dake nuna ya kamu da cutar Covid-19. Dan uwan nata ya fada mata cewa ya jajje gwaje-gwaje na cutar a Kalamazoo amma sai dai ya dawo a sakamakon kin yi masa gwajin da asbitin suka kiyi. Sai dai yar uwar tashi bata bayyana sunan asbitin da suka ki yimasa gwajin. A karshe jami'ar ta taya yar u...
Idan da ranka zaka kasha kallo wata kyanwa yar asalin kasar Belgium ta kamu da cutar Numfashi wanda aka fi sani da Coronavirus

Idan da ranka zaka kasha kallo wata kyanwa yar asalin kasar Belgium ta kamu da cutar Numfashi wanda aka fi sani da Coronavirus

Kiwon Lafiya
Ita dai wannan kyanwa yar asalin kasar Belgium ta kamu da cutar Numfashi wanda aka fi sani da Coronavirus. Kyanwar dai ba'a bayyana shekaraun ta ba, sai dai kamar yadda majiyar Brussels Times reported ta rawaito tace, wannnan kyanwa ta kamu da iftila'in annobar cutar ne daga gun mai ita Wanda aka rawaito yana dauke da cutar kamar yadda majiyar ta shaida. Bayan gwajin da akai wa kyanwar an tabbatar itama ta kamu da cutar bisa ga wasu alamomi da suka fara bayyana a jikin ta, inda aka samu tana yawan amai gami da yawan gudawa babu kakkautawa a cewar wani kwararran likita mai suna Steven Van Gucht wanda mai bincike ne a asbitin Jami'ar Ghent University’s a fannin magun-guna. A cewarsa ya duwar cuta tsakanin mutum da kuma dabbobi abu ne mai saukin gaske. Sai dai harzuwa yanzu baya g...
Mutum na farko da ya samu mafi karancin maki a Tarihin Jamb

Mutum na farko da ya samu mafi karancin maki a Tarihin Jamb

Uncategorized
Mutum na farko da ya samu mafi karancin maki a Tarihin Jamb. Yaron da aka fi sani da Salaudeen Farouq ya zama mutum na Farko da ya samu mafi karancin maki a Jarrabawar Jamb. An bayar da rahoton cewa yaron Wanda ya rubutu jarabawar a ranar 18th ga watan Maris 2020 ciki har da Harshen Turanci, Lissafi, Physics, da Chemistry wanda ya samu maki gaza da 25 ya samu maki 10 a harshan turanci maki 5 a shauran darusan. Salaudeen yaro ne dan shekara 18 wanda a yanzu haka yana SS3 kuma yana halartar Al-Fatilah Group of Schools, dake Kano. Yaron wanda yace iyayan sa ne suka tursasa masa zana jarabawar a sakamakon ganin abokan karatunsa duk sun shirya zana jarabawar a shekarar.
Wata Sabuwa: Kwayar Cutar Yunwa Tafi Illata Yan Najeriya Sama da Coronavirus A cewar Sarkin Musulmi

Wata Sabuwa: Kwayar Cutar Yunwa Tafi Illata Yan Najeriya Sama da Coronavirus A cewar Sarkin Musulmi

Kiwon Lafiya
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar II yayi Kira da gwamnati da ta dauki matakan gaggawa don inganta rayuwar 'yan Najeriya, yana mai cewa "cutar yunwa" tana kashe' yan Najeriya fiye da tsoron cutar COVID-19 (Coronavirus).   Mai alfarma Sarkin wanda ya yi jawabi a taron farko na Majalisar Addinai ta Najeriya (NIREC), a Abuja, ranar Alhamis, inda yace ko da yake, Cutar Coronavirus na kashe daruruwan mutane a fadin duniya, "   Amma a cewarsa cutar yunwa" ita ce babbar cutar da take kashe 'yan Najeriya.   Ya kuma Kara da cewa shin akwai kwayar cutar da ke kashe 'yan Najeriya da ta fi Coronavirus girma. Inda ya bayar da amsa da cewa wannan kwayar cutar itace yunwa.   A cewarsa kwayar cutar yunwa tana da matukar tsanani. Inda ya bayyana da cewa ...