fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Covid19 Gombe

Gwamnatin jihar Gombe ta sallami mutum 20 da aka killace a jihar a sakamakon kamuwa da cutar Korona

Gwamnatin jihar Gombe ta sallami mutum 20 da aka killace a jihar a sakamakon kamuwa da cutar Korona

Kiwon Lafiya
An sallami mutanen ne bayan an yi musu gwaji har sau biyu an ga ba sauran cutar a tare da su. Da yake bayani ga manema labarai kafin sallamar majinyatan, Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Ahmed Muhammad Gana, ya ce mutanen 20 na cikin mutum 103 da aka tabbatar suna dauke da cutar kuma za a sallami 10 daga Asibitin Cututtuka Masu Yaduwa na Farfesa Idris Muhammad da ke garin Kwadom a yankin karamar hukumar Yamaltu Deba da kuma wasu 10 dake Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya (FTH) da ke Gombe.   Kwamishinan, wanda ya yi bayanin a madadin shugaban kwamitin yaki da cutar, ya nemi hadin kan yan jarida a jihar wajen yada labarai masu inganci kan wannan cutar ba tare da yada labarin da zai jawo tashin hankali ba.   Ya kuma bukaci al’ummar gari su ma su bai wa yan kwami...
Gwamnan jihar Gombe ya ce masu dauke da cutar COVID-19 da suka gudanar da zanga-zanga a jihar Gombe ba ‘yan asalin jihar bane

Gwamnan jihar Gombe ya ce masu dauke da cutar COVID-19 da suka gudanar da zanga-zanga a jihar Gombe ba ‘yan asalin jihar bane

Kiwon Lafiya
Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya ce, masu dauke da cutar COVID-19 da suka gudanar da zanga-zanga a jihar Gombe ba ‘yan asalin jihar bane; baki ne daga wasu jihohin da aka gwada su a Gombe kuma aka tabbatar sun harbu da cutar, a saboda haka dole aka killace su a can.   Kwamishinan yada labaran jihar ta Gombe, Alhaji Alhassan Kwami ne ya tabbatar da hakan yayin wata tattaunawa da ya yi da gidan rediyon Freedom, inda ya kara da cewa wadanda suka gudanar da zanga-zangar baki ne daga jihohin Kano, Legas da kuma Ogun.   Kwamishinan ya ci gaba da cewa, a kokarinsu na ganin cewa cutar bata fantsama ba a jihar ta Gombe ne ya sanya suka dauki gabarar yi wa duk wani wanda ya shigo cikin jihar gwaji, kuma ta haka ne suka samu mutane har guda 101 sun harbu.  ...