Hukumar lafiya ta jihar kano ta sanar da samun karin mutum 13 da suka harbu da cuta mai sarke Numfashi hakanan hukumar ta sallami karin mutum 27 da suka warke garau daga cutar.
https://twitter.com/KNSMOH/status/1361041281158426630?s=20
Jihar Kano.
A ranar Talata ne gwamnatin jihar Kano ta sanar da dage takunkumin da ta Sanya na hana buga wasanni a jihar.
Shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano, Ibrahim Galadima ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Abbati Sabo , ya fitar a Kano.
Sai dai rahoton da hukumar ta fitar ta ce, An bar masu wasanni suna fita a tisaye amma babu hada sauran wasanni da zai haifar da cunkoso.
Haka zalika Galadima ya jawo hankali kan ya zama wajubi da a cigaba da kula da ka'idojin cutar Covid-19.
Ma'aikatar lafiya ta jihar kano ta bayyana Kara samun adadin mutum 5 masu dauke da cutar coronavirus wanda kuma ta tabbatar da sallmar mutum 2 wanda suka warke daga cutar.
Sanarwar hakan tazo ne ta cikin shafin hukumar dake dandalin sada zumunci na twita.
https://twitter.com/KNSMOH/status/1263235914748346369?s=20
Ya zuwa yanzu jihar ta sallami adadin mutum 121.
Gwamnatin tarayya a ranar litinin ta kara tsawaita dokar kulle har tsawan sati biyu.
Shugaban kwamitin shugaban kasa kan cutar Corona PTF Boss Mustapha ne ya sanar da hakan, a yayin ganawa da mambobin kwamitin a Abuja.
Yanzu dai Jihar kano zata cigaba da zama a kulle har na tsawan sati 2, har zuwa nan da watan yuni.
Idan zaku tuna Shugaban kasa Buhari ya bada umarnin rufe jihar kano tsawan sati biyu a makwannin baya, a sakamakon yawan karuwar masu cutar corona da jihar ke fuskanta.
Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kebe kananan yara almajiri 2000 don dakile yaduwar cutar COVID-19 a cikin jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar, Aminu Tsanyawa, ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis a wurin bude horarwa ga rukunin jami'an lafiya da zasu na kula da yaran da aka kebe, a cibiyoyin kebewar.
Dokta Aminu Tsanyawa ya ce, an zabi masu horon ne daga likitoci ma’aikatan jinya, ma’aikatan kiwon lafiya na yankin da kuma masana kimiyyar gwaje-gwaje domin gwada tare da tantance yaran almajiri a sansanoninsu da ke kananan hukumomin Kiru, Gabasawa da Karaye na jihar.
Ya yi bayanin cewa almajiris, gami da wadanda aka dawo da su daga wasu jihohin zuwa Kano, za a yi masu gwajin COVID-19.
Jihar kano yanzu adadin masu cutar ya kusan Kai dubu a jihar.
Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a wani zama da ya yi da Sarakunan jihar guda biyar masu daraja ta daya, ya yi wa sarakunan bayani dalla-dalla kan matakan da gwamanti ta dauka wajen hidimar yaki da cutar COVID-19 a jihar.
Ganduje ya kuma bukaci sarakunan da su isar da sakon matakan da gwamnati ta dauka na yaki da COVID-19 a Kano ga masarautunsu da kuma al’ummarsu baki daya.
“Bukatarmu ita ce na mu dakile yadda cutar ke yaduwa a jiharmu, wannan kuma shi ne ya sa muka ga ya dace mu yi wannan zaman don tattauna hanyoyin da za su zame mana mafita.
“COVID-19 ta shafi duk wani bangare na rayuwarmu tun daga kan addininmu, al’adunmu, tattalin arzikinmu da ma zamantakewarmu,” inji Ganduje.
Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, a madadin ragowar sarakun...
Gwamnatin jihar kano ta umarci kotun tafi da gidan ka da tafara hukunta duk wanda aka kama bai sanya abun rufe baki da hanci ba da aka fi sani da Face Mask don kariya daga cutar corona.
Gwamna Abdullahi ganduje ne ya bayyana hakan a ranar lahadi a lokacin da kwamitin karta kwana kan cutar Covid-19 ke bayanin halin da ake ciki a game da cutar a jihar.
Ya kara da cewa domin kariya daga cutar Gwamnati ke rarraba abun rufe hanci kyauta a duk kan kananan hukumomi 44 dake fadin jihar.
A ranar Lahadin da ta gabata jihar Kano ta kara sallamar wasu masu dauke da cutar COVID-19 guda goma wadanda aka tabbatar da warkewar su daga cutar bayan gwaji da akai musu har sau 2.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba shine wanda ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce, marassa lafiyar sun murmure sosai kuma an gwada su basa dauke da cutar a halin yanzu.
Sanarwar ta ce jihar ta kuma sami asarar rayuka 3 a ranar Asabar wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu daga cutar coronavirus zuwa 21.
A karshe ya hori al'umma da suna bin matakan kariya wajan tsaftar hannu da kuma sanya takunkumin rufe hanci don kariya daga cutar.