
Idan Gemun dan uwanka ya kama da Wuta..:An tura jami’an tsaro su kare rumbunan adana kaya tare da kaddarorin jama’a a jihar Katsina
Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Katsina ta bayyana cewa ta tura jami’an ta ne don kare rumbunan adana kaya da kadarori daga hare-haren‘ yan daba a jihar.
Mai magana da yawun ta, Sufeto Gambo Isah, ya fadawa The Nation cewa rundunar, tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro, sun dauki kwararan matakai don kare kadarorin jama'a da na masu zaman kansu da kuma rayuka.
Ya kara da cewa hukumomin tsaro sun kammala shirye-shiryen aiki a kan titunan Katsina da na kananan hukumomin da za a fara daga yau.
Ya ba da tabbacin cewa za a rika yin sintiri a kan tituna da manyan wurare don haka don tabbatar da isasshen kariya ga rayuka da dukiyoyi.
Ya ce: “Ee duk rumbunan ajiyar kaya a cikin jihar kuma hakika sauran kadarori suna da cikakken tsaro. Hukumomin tsaro za su fara aiki da s...