
Darakta Janar na hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC)ya bayyana takaicinsa bisa yadda gwamnatin jihar Kogi ta ki karbar tayin da hukumar NCDC ta yi mata na ta shiga jihar don tantance matsayin cutar COVID-19 a cikin jihar
Shugaban hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC), Chikwe Ihekweazu, ya bayyana takaicinsa bisa yadda gwamnatin jihar Kogi ta ki karbar tayin da hukumar NCDC ta yi mata na ta shiga jihar don tantance matsayin cutar Corona a cikin jihar.
Jihohin Kogi da ta Cross Rivers su ne kawai jihohi kwaya biyu da ba a samu fantsamar cutar COVID-19 a cikinsu ba.
An jiyo gwamnatin jihar Kogi na zargin wai ana kokarin kakaba mata cutar COVID-19 a cikin jiharta ta dole-dole.
A yayin da tawagar NCDC ta isa jihar Kogi a daren Alhamis din da ta gabata, sai Gwamna Yahaya Bello ya umarni da ko dai a killace tawagar na tsawon kwanaki 14, ko kuma tawagar ta fita ta bar masa jiharsa.
A bayanin da daraktan NCDC ya fitar ranar Juma’ar da ta gabata, ya bayyana matukar takaicinsa...