fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: Covid19/madagaska

Hukumar dake kula da lafiya ta yankin afirka ta yi fatali da maganin cutar corona da kasar Madagaska ta samar

Hukumar dake kula da lafiya ta yankin afirka ta yi fatali da maganin cutar corona da kasar Madagaska ta samar

Kiwon Lafiya
Da alamu na nuni da cewa Maganin Madagaska bai karbu gun ECOWAS ba   A yayin da kasashen nahiyar Afirka ke ci gaba da rububin karbar maganin gargajiyar COVID-19 na kasar Madagaska, hukumar da ke kula da kiwon lafiya ta yankin yammacin africa ta nesanta kanta da maganin.   Akalla kasashe uku ne dai a yankin yammacin Afirkan da suka hadar da Laberiya da Guinea Bissau da kuma Jamhuriyar Nijar, suka karbi maganin na kasar Madagaska. Kasar da ke takama da Samar da maganin gargajiy, da nufin neman mafita a cikin rikicin coronavirus da ke kara kamari. Cikin wata sanarwar data fitar dai hukumar tace ba ta bayar da izinin karbo maganin daga kasar ta Madagaskan ba, sannan kuma ba ta nuna amincewarta bisa amfaninsa tsakanin al'ummar yankin na yammacin Afrirkan ba.