fbpx
Friday, December 2
Shadow

Tag: Covid19 Nigeria

Sabbin mutum 566 sun harbu da cutar coronavirus/covid-19 a Najeriya jimulla 25,133

Sabbin mutum 566 sun harbu da cutar coronavirus/covid-19 a Najeriya jimulla 25,133

Kiwon Lafiya
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka NCDC ta sake fidda sanarwar kara samun adadin mutum 566 wanda suka harbu da cutar coronavirus a fadin kasar. Sanarwar wanda hukumar ta wallafa ta cikin shafinta dake kafar sadarwa a ranar jLitinin 29 ga watan Yunin shekara ta 2020. Haka zalika hukumar ta zayyana jahohin da aka samu karin masu cutar wadanada suka hada da: Lagos-166 Oyo-66 Delta-53 Ebonyi-43 Plateau-34 Ondo-32 FCT-26 Ogun-25 Edo-24 Imo-15 Bayelsa-13 Benue-12 Gombe-11 Kano-11 Kaduna-11 Osun-8 Nasarawa-7 Borno-5 Katsina-2 Anambra-2. https://twitter.com/NCDCgov/status/1277729455528652810?s=20 Bayan haka cibiyar ta bada rahoton sallamar adadin mutum 9,402 sannan kuma an samu.mutuwar mutum 573 a fadin kasar.
Covid-19: Gwamnatin tarayya ta janye dokar hana shiga jahohin Kasar

Covid-19: Gwamnatin tarayya ta janye dokar hana shiga jahohin Kasar

Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya ta cire dokar data sanya na hana shiga jahohin kasar a sakamakon bullar cutar Coronavirus.   Sanarwar hakan na kunshe ne ta cikin bayanin da sakataran gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya gabatar ga manema labarai a taron kwamaitin yaki da cutar coronavirus da ake gabatarwa yau da kullum a birinin tarayya Abuja. Boss Mustapha wanda shine shugaban kwamitin ya bayyana cewa matakin zai fara aiki ne daga 1 gawatan Yuni.
Covid-19: Ya zuwa  yanzu Najeriya ta sallami adadin mutum 9007 bayan samun karin 490

Covid-19: Ya zuwa yanzu Najeriya ta sallami adadin mutum 9007 bayan samun karin 490

Kiwon Lafiya
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka NCDC ta sake fidda sanarwar kara samun adadin mutum 490 wanda suka harbu da cutar coronavirus a fadin kasar. Sanarwar wanda hukumar ta wallafa ta cikin shafinta dake kafar sadarwa a ranar Lahadi 28 ga watan Yunin shekara ta 2020. Haka zalika hukumar ta zayyana jahohin da aka samu karin masu cutar wadanada suka hada da: Lagos-118 Delta-84 Ebonyi-68 FCT-56 Plateau-39 Edo-29 Katsina-21 Imo-13 Ondo-12 Adamawa-11 Osun-8 Ogun-8 Rivers-6 Kano-5 Enugu-3 Bauchi-3 Akwa Ibom-3 Kogi-1 Oyo-1 Bayelsa-1 https://twitter.com/NCDCgov/status/1277368328273760262?s=20 Bayan haka cibiyar ta bada rahoton sallamar adadin mutum 9,007 sannan kuma an samu.mutuwar mutum 565 a fadin kasar.
An samu karin mutum 684 wanda suka harbu da cutar coronavirus/covid-19 a Najeriya

An samu karin mutum 684 wanda suka harbu da cutar coronavirus/covid-19 a Najeriya

Kiwon Lafiya
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka NCDC ta sake fidda sanarwar kara samun adadin mutum 684 wanda suka harbu da cutar coronavirus a fadin kasar. Sanarwar wanda hukumar ta wallafa ta cikin shafinta dake kafar sadarwa a ranar juma'a 26 ga watan Yunin shekara ta 2020. Haka zalika hukumar ta zayyana jahohin da aka samu karin masu cutar wadanada suka hada da: Lagos-259 Oyo-76 Katsina-69 Delta-66 Rivers-46 Ogun-23 Edo-22 Osun-22 Ebonyi-21 FCT-20 Kaduna-16 Ondo-10 Imo-9 Abia-9 Gombe-5 Plateau-4 Bauchi-4 Ekiti-2 Anambra-1. Bayan haka cibiyar ta bada rahoton sallamar adadin mutum 8,253 sannan kuma an samu.mutuwar mutum 554 a fadin kasar.
Covid-19: “Kar kubude Makarantu da guraran kallan ball lokaci baiyi ba – Gwamnatin tarayya ta gargadi jahohin kasar

Covid-19: “Kar kubude Makarantu da guraran kallan ball lokaci baiyi ba – Gwamnatin tarayya ta gargadi jahohin kasar

Kiwon Lafiya
A ranar litinin gwamnatin tarayyar Najeriya ta aike da wani gargadi ga jahohin kasar kan kin bude makarantu guraran filin ball hadi da gidajan kallo. Wannan gargadi na kunshe ne ta cikin bayanin da shugaban kwamitin yaki da cutar Coronavirus kuma sakatare janar na shugaban kasa Boss Mustapha yayi a ranar litinin, a Abuja. Kwamitin ya shawarci jahohi da su mutunta yar'jejeniyar haka zalika a cewar sa, "sam lokaci baiyi ba na bude makarantu da sauraran guraran dake tara cunkoson jama'a. A satin da ya gabata gwamnatin jihar kano ta sanar da bude gidajan kallo, baya ga haka itama  jahar Cross River na shirin bude makarantun jahar dan cigaba da gudanar da karatu.
Ministan kula da ayyukan jinkai Sadiya Umar Farouk ta ki amsa gayyatar da kwamitin majalisar kasa yai mata a karo na 4

Ministan kula da ayyukan jinkai Sadiya Umar Farouk ta ki amsa gayyatar da kwamitin majalisar kasa yai mata a karo na 4

Siyasa
Ministar kula da ayyukan jinkai, Hajiya Sadiya Umar Farouk a ranar Litinin, ta ki amincewa a karo na hudu, bisa gayyatar da kwamitin Majalisar Wakilai yai mata domin yin bayani game da yadda ofishinta ya gudanar da rarraba kudaden da aka kebe don talafawa marasa galihu a sakamakon barkewar cutar coronavirus a Najeriya. An nemi ministar ta bayyana a gaban kwamitin majalisar don ta yi bayani dalla-dalla yadda aka rarraba kudaden da aka bai wa ma'aikatar da cibiyoyi da hukumomin da ke karkashin kulawarta. Sai dai rashin amincewar amsa gayyatar da majalisar taiwa ministar, ya saba wa sashi na 4, 81, da 88 na kundin tsarin mulki na shekarar 1999. Wanda ya baiwa majalisar ikon yin bincike a kan kowa wanda ya hada da Shugaban Tarayyar kasa da kuma Ministocinsa da shugabannin hukumomin gwamn...
Wasu mambobi 5 na majalisar jihar Gombe sun kamu da cutar coronavirus/covid-19

Wasu mambobi 5 na majalisar jihar Gombe sun kamu da cutar coronavirus/covid-19

Kiwon Lafiya
Rahotanni sun bayyana cewa Mambobin majalisar jahar Gombe su kimanin mutum 5 sun harbu da cutar coronavirus/covid. Wata majiya mai tushe ta fadawa Solacebase a ranar Litinin inda kuma shafin Hutudole ya labarto daga majiyar da cewa mambobin suna daga cikin mutum 16  da aka tabbatar sun kamu da cutar Covid-19 a jihar a ranar Lahadi.   Majiyar ta ce daya daga cikin mambobin da suka kamu da cutar ta tabbatar wa wakilinmu cewa mambobi biyar din sun hada da wasu manyan jami’an majalisar. Haka zalika An kuma ruwaito cewa wani memba na majalisar zartarwa na jihar shima ya kamu da cutar coronavirus. Sai dai har yazuwa yanzu kwamitin yaki da cutar Covid-19 bai tabbatar da lamarin kamuwar manyan jami'an gwamnatin jihar ba, harzuwa wannan lokaci.
Bayan samun karin mutum 348 yanzu masu cutar coronavirus a Najeriya sun  haura dubu 11

Bayan samun karin mutum 348 yanzu masu cutar coronavirus a Najeriya sun haura dubu 11

Kiwon Lafiya
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka NCDC ta fitar da sanarwar samun mutum 348 wanda suka harbu da cutar covid-19 a Najeriya,   Wanda ya zuwa yanzu adadin masu cutar ya kai 11,166.   An samu karin masu dauke da cutar daga jahohin:   Lagos-163 FCT-76 Ebonyi-23 Rivers-21 Delta-8 Nasarawa-8 Niger-8 Enugu-6 Bauchi-5 Edo-5 Ekiti-5 Ondo-5 Gombe-5 Benue-4 Ogun-2 Osun-1 Plateau-1 Kogi-1 Anambra-1. https://twitter.com/NCDCgov/status/1268315252707516423?s=20 Ya zuwa yanzu an sallami mutum 3329
Bayan samun karin mutum 284 ya zuwa yanzu adadin masu dauke da cutar coronavirus/covid-19 ya kai 6677 a Najeriya

Bayan samun karin mutum 284 ya zuwa yanzu adadin masu dauke da cutar coronavirus/covid-19 ya kai 6677 a Najeriya

Kiwon Lafiya
Cibiyar dakile ya duwar cututtuka ta sake fidda sanarwar kara samun adadin mutum 284 wanda hukumar ta tabbatar sun kamu da cutar Covid-19.   Jahohin da aka samu karin sun hada da 199-Lagos 26-Rivers 19-Oyo 8-FCT 8-Borno 7-Plateau 6-Jigawa 5-Kano 2-Abia 1-Ekiti 1-Delta 1-Kwara 1-Taraba. https://twitter.com/NCDCgov/status/1263233210462416897?s=20 Ya zuwa yanzu hukumar ta sallami adadin mutum 1840 baya ga haka an samu mutuwar mutum 200 a kasar.
Covid-19: Gwamnatin tarayya ta zabtare al’bashin ma’aikatan tashar jirgin sama

Covid-19: Gwamnatin tarayya ta zabtare al’bashin ma’aikatan tashar jirgin sama

Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya ta zabtare albashin ma’aikatan tashar jirgin sama a kasar. Manajan Hukumar Kula da Filin Jiragen Sama na Najeriya a ranar 19 ga watan mayu 2020 ya ce rage albashin ya kasance ne a sakamakon rufe filin tashin jirgin saman sakamakon cutar Coronavirus da ta bulla a kasar. Jaridar Daily trust ta rawaito cewa Takardar wacce Babban Daraktan Hukumar ta FAAN, MD, Musa ya sanya wa hannu, ya ce, "Muna sanar da duk wasu ma'aikatan  cewa sakamakon karancin kudaden shiga da ake samu a sakamakon  annobar cutar coronavirus hakan na yiwuwa hukumar gudanarwa bazata iya biyan cikakken al'bashin ma'aikaci ba daga watan mayu 2020. Amma a cewar sa dazarar kudaden shiga sun inganta, hukumar zata cigaba da biyan ma'aikata hakkokin su, kamar yadda aka saba.   Idan zaku iya tunawa Shug...