
Gwamnatin Tarayya za ta gana da jihohi ranar Talata don tattaunawa kan hanyoyin sake bude makarantu
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta gana da jihohi ranar Talata don tattaunawa kan hanyoyin sake bude makarantun firamare da sakandire, kamar yadda jaridar PUNCH ta labarta mana.
Makarantu a duk fadin kasar nan na kulle, tun cikin watan Maris sakamakon barkewar cutar COVID-19 a cikin kasar wanda ya haifar da 'yan Najeriya sama da mutum 25,000, sun harbu da cutar.
Shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19, Boss Mustapha, a ranar Litinin ya ba da sanarwar sake bude makarantun, yana mai cewa hakan zai ba da damar baiwa daliban da ke karatun digiri su ci gaba da shirye-shiryen jarabawa.
Duk da umarnin da Gwamnatin Tarayya ta yi na sake buɗe makarantu, har yanzu dai ana ta duba yuwuwar hakan a yayin da gwamnatocin jihohi ke gwagwarmayar yanke hukunci kan ranakun sake buɗe makarantu...