
Cristiano Ronaldo ya bayyana farin cikinsa bayan zama dan wasan dayafi yawan kwallaye a tarihi
Cristiano Ronaldo ya zamo dan wasan dayafi yawan kwallaye a tarihi bayan ya ciwa United kwallaye uku a wasan data lallasa Tottenham daci 3-2.
Inda ya kerewa Josef Bican mai kwallaye 805 bayan nashi sun kai 807. Cristiano ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa yayi farin sosai da wannan tarihin daya kafa.
Kuma yana godiya ga duk kungiyoyin da yan wasan daya taka leda da dasu domun da babu su ba zai kafa wannan tarihi ba.