Sunday, June 7
Shadow

Tag: Cristiano Ronaldo

Ji abinda Messi yace da aka tambayeshi zai ba Cristiano Ronaldo kwallo idan suka buga wasa tare?

Ji abinda Messi yace da aka tambayeshi zai ba Cristiano Ronaldo kwallo idan suka buga wasa tare?

Uncategorized, Wasanni
Kaftin din Barcelona Lionel Messi ya kasance abokin hamayyar tauraron Juventus Cristiano Ronaldo fiye da shekaru goma da suka gabata.   Manema labarai Mundo Deportivo sun tambaya Messi cewa shin idan suka yi wasa tare da Ronaldo a kungiya daya zai bashi kwallo?, sai Messi yace yana tunanin hakan, daga baya kuma sai yace eh zai bashi. Ronaldo ya cika shekara ta 35 a watan fabrairu kuma yana kokari sosai a wannan kakar wasan yayin da yayi nasarar jefa keallaye 25 a wasanni guda 32 daya buga. Kuma tsohon tauraton Madrid din yayi nasarar cin kwallo a wasanni har guda 11 a jere a wannan kakar wasan.   Shi kuma Messi yayi nasarar cin kwallaye guda 24 kuma ya taimaka wurin cin kwallye guda 16 a wasanni guda 31 daya buga.     Messi ya yaba Cristiano ...
Hotuna da Bidiyo:Juventus sun dawo Atisaye

Hotuna da Bidiyo:Juventus sun dawo Atisaye

Wasanni
Kungiyar Kwallon kafa ta kasar Italiya, Juventus sun dawo Atisaye a shirye-shiryen da kungiyar ke yi na dawowa buga gasar Serie A bayan hutun dole da aka yi saboda cutar Coronavirus. Tauraron kungiyar, Cristiano shima ya kammala killacewar da aka masa ta kwanaki 14 bayan dawowa daga kasarsa ta Portugal. Kasar Italiya taga daya daga cikin yanayin cutar Coronavirus/COVID-19 mafi muni inda cutar ta kashe mutane da yawa. Saidai ga dukkan alamu al'amura sun kama hanyar dawowa daidai. https://twitter.com/juventusfcen/status/1262805217168457728?s=19 A hotunan kasa kuma Ronaldo ne a cikin motarsa yayin da ya je yin gwajin lafiyarsa.    
Ronaldo zai cigaba da yin atisayi tare da sauran abokan aikin shi yayin da suke shirin fara yin atisayin a kungiyance

Ronaldo zai cigaba da yin atisayi tare da sauran abokan aikin shi yayin da suke shirin fara yin atisayin a kungiyance

Wasanni
Cristiano Ronaldo ya koma kasar shi ta Portugal bayan sun buga wasan su na karshe kafin a dakatar da wasannin kwallon kafa tsakanin su da inter, yayin da suka yi nasarar jefa kwallaye guda biyu a wasan. Gobe litinin 19 ga watan mayu Cristiano Ronaldo zai cika kwanaki 14 na killace kuma zai cigaba da atisayi tare da sauran abokan aikin shi amma ba'a kungiyance ba. Tsohon tauraron Madrid din ya kasance tare da iyalan shi a kasar shi ta Portugal har na tsawon watannin biyu, daga baya kuma ya koma kasar Italia yayin daya ke killace kanshi har na tsawon kwanaki 14. Gwamnatin kasar Italia har yanzu suna tattaunawa gami da yadda yan wasa zasu cigaba da yin atisayi a kungiyance saboda kungiyoyin sun zabi su cigaba da buga wasannin gasar Serie A daga ranar 13 ga watan yuni idan h...
Hotuna da Bidiyo: Cristiano Ronaldo ya Bude gidan adana kayan Tarihinsa

Hotuna da Bidiyo: Cristiano Ronaldo ya Bude gidan adana kayan Tarihinsa

Uncategorized
Tauraron dan kwallon kafar kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa,Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa ya bude gidan tarihinsa.   Ronaldo ya bayyana cewa, ya saka kayan kwallonsa da nasarorin daya taba samu da kyautukan da aka taba bashi na kwallon kafa.   Ronaldon ya saka bidiyon dakin adana kayan tarihin nasa a shafinshi na sada zumunta inda tuni masiyansa suka fara bayyana farin cikinsu akai.     https://www.instagram.com/p/CAVhXr4AiFV/?igshid=1d1vdcqate6cb Ronaldo dai dama yana da gurin sayar da kayan sawa da otal wanda yake kasuwanci dasu.
Roberto Carlos: Ronaldon Brazil ne zakaran kwallon kafa kuma ba za’a taba hada shi da Cristiano Ronaldo, Messi ko Neymar ba

Roberto Carlos: Ronaldon Brazil ne zakaran kwallon kafa kuma ba za’a taba hada shi da Cristiano Ronaldo, Messi ko Neymar ba

Uncategorized
Roberto Carlos yace ba za'a kara samun wani Ronaldo ba bayan abokin aikin shi na kasar Brazil, kuma ba za'a taba danganta shi da Cristiano ba ko Messi da Neymar saboda shi na da banne. Bayan Ronaldo ya tabbar ma duniya cewa shi kwararren dan wasan a shekara ta 1996/1997 lokacin yana kungiyar Barcelona, ya fara fama da raunika a gwiwar shi har na tsawon shekaru biyar. Ronaldo ya samu cikakkiyar lafiya a lokacin daya lashe gasar kofin duniya a shekara ta 2022. Kuma jaruntakar da yayi a kasar Japan da South Korea ne yasa kungiyar Real Madrid suka siye shi, kuma yayi wasa tare da Luis Figo da Zinedine Zidane. Ronaldo yayi wasa a Real Madrid har na tsawon shekaru biyar kuma yayi aiki tare da dan kasar shi Carlos a kungiyar. Carlos yace Ronaldo yayi fice sosai a duniyar wasa...
Messi da Ronaldo sun bayyana cewa suna kewar junan su yayin da Messi ya kara da cewa Madrid sun yi babban rashi

Messi da Ronaldo sun bayyana cewa suna kewar junan su yayin da Messi ya kara da cewa Madrid sun yi babban rashi

Wasanni
Tauraron Juventus Cristiano Ronaldo da kaftin din Barcelona Lionel Messi sun kasance abokan hamayya fiye da shekaru goma da suka gabata kuma ana masu kirarin zakarun yan wasan kwallon kafa na duniya baki daya. Cristiano Ronaldo mai shekaru 35 a koda yaushe yana karyata maganar da mutane su keyi na cewa shi da abokin hamayyar shi sunawa juna adawa. Dan wasan Juventus din yace Messi yana jin irin abin da yake ji akan hamayyar su kuma yana kewar shi sosai tun da ya bar Madrid a shekara ta 2018. Cristiano Ronaldo yace yana sha'awar yadda Messi yake yin wasa kuma Messi yace bai ji dadin barin gasar La Liga da yayi ba saboda yana son gasar da suke yi a tsakanin su. Bayan Ronaldo ya bar kungiyar Madrid, Messi yace yana jin dadin wasa tare da shi kuma zai yi kewar shi sosai yay...
Karanta Abinda ke kara tabbatar da cewa Cristiano Ronaldo shine zakaran wasan kwallon kafa na duniya baki daya

Karanta Abinda ke kara tabbatar da cewa Cristiano Ronaldo shine zakaran wasan kwallon kafa na duniya baki daya

Wasanni
Cristiano Ronaldo yana daukar albashin euros 500 a kowane mako kuma yana samun kudade daga kamfanin Nike, Armani, Kfc, Herbalife da kuma kanfanin shi na saida kayan sawa da takalma. kuma yana bayar da tallafi sosai ga mabukata. Ronaldo yana da masoya da kuma makiya saboda ba kowa bane ya san irin Alkheirin da yake yi. Zaka iya/zaki iya yin musu akan cewa ragin albashin da aka yiwa yan wasan kwallon kafa baya damun Cristiano Ronaldo. Ba kowane dan wasa bane ya yarda da ragin albashin da aka yi masu ba, Amma Ronaldo shi ya jagoranci tafiyar yayin daya karbi ragin albashin watannin hudu. Kuma hakan zai sa ya rasa euros miliyan 3.8.  Cristiano da wakilin shi Mendes sun bayar da tallafin euros miliyan daya ga asibitocin kasar Portugal, kuma abokin aikin shi na Portugal Silva yace
Video: Barewa ba za tai gudu ba danta yayi rarrafe:Kalli Cristiano Ronaldo na buga kwallo da dansa

Video: Barewa ba za tai gudu ba danta yayi rarrafe:Kalli Cristiano Ronaldo na buga kwallo da dansa

Wasanni
Tauraron dan kwalon kafar kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa,Cristiano Ronaldo kenan a wannan hoton bidiyon inda yake buga kwallo da dansa. Ronaldo wanda tuni ya koma kasar Italiya dan fara buga wasannin Serie A bayan dakatarwar da aka yi saboda Coronavirus/COVID-19 yana killace da kansa ne na tsawon kwanaki 14 kamar yanda doka ta tanada. https://www.instagram.com/p/CAGQeTYg2Ny/?igshid=1apllz302kcee Ronaldo ya saka hoton bidiyon a shafinsa na Instagram inda ya mai taken Barewa ba za tai gudu ba danta yayi rarafe.
Vinicious na bin tsarin atisaye irin na Cristiano Ronaldo

Vinicious na bin tsarin atisaye irin na Cristiano Ronaldo

Wasanni
Wani Shugaba kuma kochin Atisaye mai suna Thiago Lobo yana tare da Vinicious a gidan shi na Madrid a watannin da suka gabata, shugaban yana lura da yanayin abincin da Vinicious yake ci kuma yana sa dan wasan yana cin abinci mai gina jiki. Thiago Lobo yana kokari wajen mayar da Vinicious dan wasan mai karfi da kuma kuzari. Dan wasan yana bin tsarin atisayin da Cristiano Ronaldo yake yi domin ya zamo zakaran dan wasan kwallon kafa na duniya. Lobo yana cikin mayan kochinan atisayi na kasar Brazil kuma yayi aiki tare da Santos da Gabriel a Inter. https://www.instagram.com/p/B-m0xTroVam/?igshid=1v9dwl2aptfrv Vinicious ya kira shi ya zo Madrid domin suyi aiki tare bayan ta samu rauni a wasan da suka buga da Ajax, kuma domin ya dawo akan lokaci kafin a fara buga gasar ...
Cristiano Ronaldo ya koma kasar Italia yayin da nahiyar turai ke shirin dawowa buga kwallon kafa: Kalli jerin gwanon motocin da suke take masa baya, kamar wani Sarki

Cristiano Ronaldo ya koma kasar Italia yayin da nahiyar turai ke shirin dawowa buga kwallon kafa: Kalli jerin gwanon motocin da suke take masa baya, kamar wani Sarki

Wasanni
Cristiano Ronaldo ya koma kasar Italia ranar litinin a jirgin shi na kanshi amma sai dai dan wasan zai killace kanshi na tsawon kwanaki 14 kafin ya cigaba da atisayi a kungiyar shi ta juventus.   Juventus sun bukaci gabadaya yan wasan su da suka bar Italia dasu dawo domin su cigaba da yin atisayi. Dan wasan mai shekaru 35 ya koma garin su na Madeira a lokacin da cutar Covid-19 tayi kamari a kasar Italia amma yanzu ya dawo, kamata yayi ace sai ranar 18 ga watan mayu zai koma Italian, Amma yanzu an sassauta masu dokar an basu damar cigaba da atisayin daga ranar 4 ga watan mayu. A cewar wani dan jarida na kasar Italia Giovanni Albanese, ba za'a a bar Ronaldo ya mu'amalanci abokan aikin shi ba har sai ya killace kanshi na tsawon kwanaki 14. Yan wasa sun fara yin atisayi ...