fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Cronavirus-COVID-19

Yadda Kamfanin Dangote ta tilasta wa ma’aikatanta aiki dole cikin yanayin dokar ‘Kullen Korona’ har wasu suka kamu da cutar

Yadda Kamfanin Dangote ta tilasta wa ma’aikatanta aiki dole cikin yanayin dokar ‘Kullen Korona’ har wasu suka kamu da cutar

Kasuwanci
Gwamnatin Najeriya da mutanen kasar musamman mazauna garin Legas sun kasa kunne da zura idanu domin ganin ranar da za a kaddamar da matatar mai mallakin attajiri, Aliko Dangote da yake ginawa a garin Legas.     Ana sa ran za a kammala aikin gina wannan matata tuna shekarar da ta gabata, wato 2019.   A wani bincike mai zurfi da bin diddigi da PREMIUM TIMES ta yi ta bankado yadda mahukuntan wannan kamfani suka yi kunnen uwar-shegu da dokokin dakile yada cutar CORONAVIRUS da aka saka a kamfanin ta hanyar tilasta wa ma’aikata dole su yi aiki ba tare da an sanar musu su da kayan samun kariya daga kamuwa da kwayoyin cutar ba.     Sannan duk da sanin yadda aka ci gaba da ayyuka a wannan katafaren kamfani gada-gadan a lokacin da aka saka dokar h...
Kamfanin MTN ya baiwa masu amfani da layin garabasa saboda Coronavirus/COVID-19

Kamfanin MTN ya baiwa masu amfani da layin garabasa saboda Coronavirus/COVID-19

Kiwon Lafiya
Ministan sadarwa Sheikh isa Ali Pantami yayi kira ga kamfanonin sadarwa dasu saukakawa 'yan Najeriya a wannan halin dake ciki na matsi da cutar Coronavirus/COVID-19 ta jefa mutane inda yace su rage kudin data ko na kira.   Festus Keyamo, Karamin ministan kwadago shima yayi kira ga wadannan kamfanonin sadarwa kan su tausayawa yan Najeriya bisa wannan hali da ake ciki.   Ga dukka  alamu Kamfanin MTN ya amsa wannan kira inda ya bayar da kyautar aika sako har guda 300 ga kowane Dan Najeriya dake da layin kuma zuwa kowane layi. https://twitter.com/MTNNG/status/1245380148913770496?s=19 Tsarin zai kasance mutum na iya aika sakonni 10 kyautar har na tsawon wata 1
Obasanjo ya bayar da gidanshi a mayar dashi wajan killace msu Coronavirus/COVID-19

Obasanjo ya bayar da gidanshi a mayar dashi wajan killace msu Coronavirus/COVID-19

Kiwon Lafiya
Tsohon shugaban kasa,Olusegun Obasanjo ya bayar da tsohon gidansa dake Birnin Abeokuta na jihar Ogun dan a yi amfani dashi a matsayin gurin killace masu cutar Coronavirus/COVID-19.   Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa tuni ya mikawa gwamnatin jihar ta Ogun dan fara aiki da gidan nasa.   Me magana da yawun Obasanjon,Kehinde Akinyemi ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar ya damu da cutar ta Coronavirus/COVID-19.   Ya kuma yi kira ga duk me halin taimakawa ya taimaka a kawo karshen lamarin.   Gidan na Obasanjo na da dakuna 32 da Janareta na karya kwana
Shugaba Buhari ya killace kansa kuma yana tari akai-akai duk da cewa gwaji ya nuna bashi da Coronavirus/COVID-19

Shugaba Buhari ya killace kansa kuma yana tari akai-akai duk da cewa gwaji ya nuna bashi da Coronavirus/COVID-19

Kiwon Lafiya
Bayan da aka tabbatar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa,  Abba Kyari na da cutar Coronavirus/COVID-19 an yiwa shugaban kasa,Muhammadu Buhari gwajin cutar amma shi gwajin ya nuna bashi da cutar.   Saidai Duk da haka Sahara Reporters sunce wata majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyana musu cewa shugaba Buharin ya killace kansa sannan kuma yawan tarin da yake ya saka mutane da yawa na kusa dashi damuwa.   Hakanan an shirya gurin kebewar cutar Coronavirus/COVID-19 a cikin fadar shugaban kasar.   Cikin wanda Abba Kyari yayi mu'amala dasu bayan dawowa daga Jamus da kasar Egypt akwai Aliko Dangote da shugaban 'yan sanda, Muhammad Adamu da gwamnonin Katsina dana Kogi.   A zuwa yanzu dai mutane 44 ne suka kamu da cutar a Najeriya.