fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Dadiyata

Bamu san inda Dadiyata yake ba>>Gwamnatin Kaduna

Bamu san inda Dadiyata yake ba>>Gwamnatin Kaduna

Siyasa
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa bata san inda Abubakar Idris Usman wanda aka fi sani da Dadiyata yake ba.   Hakan ya fito ne daga bakin kwamishiniyar shari'ar jihar, A'isha Dikko yayin da take bayani kan bin doka wajan hukunta duk wanda jihar take zargi da laifi. Hutudole ya fahimci tace jihar Kaduna bata da hannu akan sace Dadiyata sannan kuma bata san inda yake ba.   Ta kara da cewa duk wanda jihar take zargin ya aikata ba daidai ba tana bin doka ne wajan hukuntashi. Hutudole ya ruwaito muku cewa ta kara da cewa amma babu wani korafi da gwamnatin jihar take dashi akan Dadiyata. https://twitter.com/GovKaduna/status/1300423563699261441?s=19
Shekara Guda Da Batan Dadiyata

Shekara Guda Da Batan Dadiyata

Siyasa
Shekara guda kenan bayan ‘batan Abu Hanifa Dadiya. Ranar 1 ga watan August 2019 wasu suka je unguwan Barnawa har gidan shi suka dauke shi. Yau kimanin shekara guda daidai kenan babu wani kamshin labari game da shi. Wannan babban kalubale ne ga jami'an tsaro, an kuma take masa hakki, sannan kuna cutarwa da kuma iyalan sa.   Kafin batan shi Abu Hanifa, marubuci ne a shafukan sada zumunta kuma yana rubutu a tsarin tsawon rai da kwalliya wato ‘blogging’ shi de ‘blogger’ dan akidar ‘Kwankwasiyya a siyasa, ya yi shura a wannan fannin. Da shi da abokan shi da suke irin wannan aikin sun sa fuskantar barazana daga hukumomin tsaron DSS wasu ma an kama su an sake daga baya. An yi ta kiraye-kirayen sakin shi daga ‘kungiyoyin kare hakkin bil adama da wasu daban, an yi ta tarukan manem...