
Bidiyo da Hotuna: Yanda Wasu suka yi Sallar Juma’a a tsaye wasu kuma suka hakura da sallar a Masallacin Dahiru Bauchi Kaduna Saboda Ruwan Sama
A yau, 28 ga watan 8 shekarar 2020 ne tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya jagoranci sallah a masallacin Dahiru Bauchi dake Tudun Wada, Kaduna.
Tun kamin a fara Sallah ruwan sama ya tsuge inda mutane dake zaune a cikin sahu suna jira a Fara Sallah, wasu suka tashi suka ruga cikin barandu da inda ake Alwala. Hutudole ya ruwaito muku cewa dalilin hakane aka matsu da yawa, ba masaka tsinke.
A haka aka tayar da Sallar saidai wasu saboda Rashin rashin isashshen wuri sun yi Sallah a tsaye yayin da wasu kuma suka hakura da Sallar. Kalli bidiyon a kasa.
https://youtu.be/OyMCx9XG6dA