fbpx
Friday, May 27
Shadow

Tag: Dambarwa

Rikici ya barke a majalisar Kano kan ‘tsige’ Sarki Sanusi

Rikici ya barke a majalisar Kano kan ‘tsige’ Sarki Sanusi

Siyasa
Rahotanni daga jihar Kano na cewa rikici ya barke a zauren majalisar dokokin jihar kan bukatar mataimakin shugaban majalisar, Hamisu Ibrahim Chidari na son gabatar da rahoton kwamitin bincike kan sarkin Kanon, Sarki Muhammadu Sanusi II.   Majalisar ta kasu gida biyu- wato da masu goyon bayan jam'iyyar APC wanda kuma sune suke goyon bayan a gabatar da rahoton, da kuma 'yan bangaren jam'iyyar PDP da ke ikirarin cewa rahoton wani yunkuri ne na gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje na son a tsige sarkin.   Bangarorin biyu sun tsunduma gardama kan wannan batu kuma bangarorin biyu sun kasa cimma matsaya, inda har shugaban marasa rinjaye a majalisar, Isyaku Ali Danja ya yi kokarin dauke sandar majalisar.   Wannan ya sa 'yan majalisar suka shiga kokawa da juna. Rahotan...
Ya kashe Budurwarsa ‘yar shekaru 14 a Katsina bayan data zargeshi da Dirka mata cikin shege

Ya kashe Budurwarsa ‘yar shekaru 14 a Katsina bayan data zargeshi da Dirka mata cikin shege

Uncategorized
Wani Matashi me suna Shafi'u Haruna dan kimanin shekaru 27 ya kashe budurwarsa bayan da aka zargeshi da dirka mata cikin shege.   Shafi'u Haruna ya ja budurwarsa, Hamsiya Lawal 'yar kimanin shekaru 14 bayan garinsu, Dorawar Natiba dake garin Birdigau karamar hukumar Kankara inda ake zarginshi da amfani da wani murgujejen Dutse wajan fasa mata kai kuma ta mutu, kamar yanda kakakin 'yansandan jihar,SP Gambo Isah ya shedarwa manema labarai.   Haruna ya aikata laifinne a watan Disambar Shekarar 2019 data gabata amma ba'a samu kamashi ba sai ranar talatar makon daya gabata.    
Dalilin da ya sa na maka Deezell a Kotu>>Maryam Booth

Dalilin da ya sa na maka Deezell a Kotu>>Maryam Booth

Nishaɗi
Fitacciyar ‘yar wasan fina-finan Hausa, Maryam Booth, ta bayyana cewa bayan shawara da da ta yi da lauyoyin, ya zama dole ta maka Deezell a kotu.   Idan ba a manta ba, a makwannin da suka gabata aka saki wani bidiyon tsaraici na dake nuna jarymar tsirara a dakin Otel tana canja kaya.   Tun a wancan lokaci mutane da dama suka rika yin tir da wannan abu da suka ga wanda ya sami wannan bidiyon tsiraici na jarumar.   Ibrahim Rufai da aka fi sani da suna Deezell ne jarumar ta zarga cewa shine yake tare da ita a wannan daki kuma shine ya dauke da wayarsa.   Daga baya ya ce ba shi bane ya yada Bidiyon sannan kuma ya shigar da kara kotu bisa zargin kazafi da aka yi masa.   Bayan haka ne Maryam ta shifar da nata karar ta neman kotu ta tilata wa...
Yadda na rika kama mijina na lalata da matan mamun sa ga shi Limamin Masallaci>>Mata

Yadda na rika kama mijina na lalata da matan mamun sa ga shi Limamin Masallaci>>Mata

Uncategorized
Uwargidan wani Limamin masallaci a jihar Legas Rebecca Yusuf ta shigar da kara kotu a garin Legas tana rokon kotu ta raba aurenta da mijinta mai suna Yusuf da ta kama sau dayawa yana lalata da matan mamumsa sa.   Matar tasa mai suna Rebecca ta bayyana cewa mijin ta Yusuf ba mutumin kirki bane domin yakan zagaya ya rudi matan mamun sa yana lalata da su.   Ya’yan Rebecca da Yusuf guda hudu ne kuma sun shekara 15 a aure.   Ta ce wata rana ta kama mijinta Yusuf yana lalata da matar wani mutumi dake sallah a masallacin da ya ke limanci.   “ Ina ganin su sai na yaga wa matar kayan dake jikinta sannan na saka ihu. Yusuf ya roke ni da na daina ihu domin kada mutane su ji mijin wannan mata ya sake ta.   Rebecca ta ce wannan ba shine karon farko...
HARKALLAR NAIRA BILIYAN 3.6: Gidan Radiyon Bauchi ta Kori manajanta saboda yin shiri kan zargin harkallar kwangilar gwamna Bala

HARKALLAR NAIRA BILIYAN 3.6: Gidan Radiyon Bauchi ta Kori manajanta saboda yin shiri kan zargin harkallar kwangilar gwamna Bala

Siyasa
Duk da cewa manajan gidan Radiyon Albarka dake Bauchi Waziri Hardawa ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ya shirya wannan shiri ne domin wayar da kan mutanen jihar a matsayiun sa na dan jarida amma kuma ashe wai hakan da yayi ba daidai bane. Hardawa ya bayyana cewa tattaunawa batun kawai akayi a filin shirin radiyon da bai sa ya ce komai ba amma kuma a karshe shine ya kwashi kashin. Albarka Radiyo mallakin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar ne kuma tsohon shugaban gidan radiyon Tarayya, Ladan Salihu. Hardawa ya kara da cewa ko a ranar da Ladan ya sallameshi a aiki ya bashi kyautar mota kuma har yanzu suna gaisawa. ” Ni na dauka a matsayina na kwararren dan jarida, ina aiki domin mutane da wayar musu da kai da kuma yada abubuwan dake faruwa da ya kamata su sani ne.” I...
An sake samun wata mata da ake zargi da auren maza biyu a Kano

An sake samun wata mata da ake zargi da auren maza biyu a Kano

Auratayya
Kotun shari’ar musulunci dake zamanta a Hotoro, ta cigaba da sauraron karar da wani tsohon Dan Sanda mai suna Abubakar Abdullahi Sheka ya shigar gabanta, yana zargin matarsa tayi sabon aure akan auren sa.   Wannan tsohon Dan sanda ya bayyanawa kotun cewa, yana neman shari’a ta taimaka masa, ta kwato masa matarsa, mai suna Khadija Isah Musa, daga hannun makocinsa da suka zauna a gidan haya mai suna Muhammad Sani Dawaye.   Tun da farko mai kara Abubakar Abdullahi ya ce ya kwanta rashin lafiya ne sakamakon wani harin Bomb da ya rutsa da shi, a yayin da yake jinya ne kuma sai mai gidan da suke hayar ya basu wa’adin tashi daga gidan.   Ita kuwa matar Khadija Isah Musa ta ce ba zata bishi su koma gidansu na gado ba, karshe tilas ya barta a gidan.   ...
BIDIYON TSARAICI: Maryam Booth Ta Maka Tsohon Saurayinta A Kotu , Ta Nemi Ya Biya Ta Miliyan 300

BIDIYON TSARAICI: Maryam Booth Ta Maka Tsohon Saurayinta A Kotu , Ta Nemi Ya Biya Ta Miliyan 300

Nishaɗi
Sananniyar jarumar finafina Hausa, Maryam Booth, ta maka tsohon saurayinta, Ibrahim Ahmed Rufai a gaban kotu sakamakon zarginsa da ta ke da yada bidiyon tsiraicinta ba tare da izininta ba kamar yadda Daily Nigeria ta ruwaito. Idan za mu tuna, makonni kadan da suka gaba ne kafafen sada zumuntar zamani suka hautsine da bidiyon tsiraicin jarumar. Lamarin da ya jawo martani da cece-kuce daga jama'a masu tarin yawa. Bayan kwanaki kadan da walllafa wannan bidiyon, jarumar ta fito ta bayyana wanda ta ke zargi da wannan aika-aikar. Ta ce tsohon saurayinta kuma matashin mawaki Deezell ne da wannan aika-aikar. A don haka ne kuwa jarumar ta sha alwashin daukar matakin shari'a a kan tsohon saurayin nata da ya ci amanarta. A karar da ta shiga a ranar 27 ga watan Fabrairun 2020 a gaban w...
Duk Wanda Ya Fitar Da Bidiyon Tsaraici Na, Sai Allah Ya Saka Min>>Safara’u Kwana Casa’in

Duk Wanda Ya Fitar Da Bidiyon Tsaraici Na, Sai Allah Ya Saka Min>>Safara’u Kwana Casa’in

Nishaɗi
Jarumar finafina Hausa wadda ta fito cikin shirin Kwana Casa'in, wacce aka fi sani da Safarau ta yi Allah wadai ga masu zaginta a kafafen sada zumunta saboda wani bidiyon ta da ya fita aka nuno ta tsirara. Jarumar ta bayyana hakan ne a wani gajeren bidiyo inda aka nuno jarumar na sharbar kuka tana cewa duk wanda ya tona asirin wani shi ma nasa ba zai rufu ba. Jarumar ta ce "abin haushi mutane sai su rinka zagin 'ya'yan mutane a soshiyal midiya? Tace ku yi ta yadawa. Duk wanda ya yi min shi ma idan Allah ya yarda kafin ya mutu sai an yi wa 'yar uwarsa". Ta kuma kara da cewa insha Allah duk wanda ya fitar da wannan bidiyon sai Allah ya saka mata.