fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Tag: Dangiwa Umar

Za ka yi ragaraga da Najeriya da irin salon mulkin ka na nuna bangaranci a nade-naden gwamnati>>Dangiwa Umar ga Buhari

Za ka yi ragaraga da Najeriya da irin salon mulkin ka na nuna bangaranci a nade-naden gwamnati>>Dangiwa Umar ga Buhari

Siyasa
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna Dangiwa Umar ya ya gargadi shugaban kasa da kakkausar murya cewa yadda yake nuna son kai da fifiko a nade-naden sa zai iya jefa Najeriya cikin halin tashin hankali mai muni.     A wata budaddiyar wasika da ya rubuta wa shugaba Buhari, Dangiwa Umar ya bayyana cewa dama kuma Najeriya na cikin rudanin rabuwar kai a yanzu.   Dangiwa ya ce Buhari ya fi nuna sonkai da bangaranci a nade-naden shugabannin rundunonin tsaron kasar nan.     Bayan haka Dangiwa ya kawo misali da yadda gwamnatin Buhari ta ci mutuncin tsohon babban maisharia na kasa Walter Onnoghen wanda dan asalin jihar Cross Rivers ne wato yankin Kudu Maso Kudu. Duk da yana da damar Buhari ya amince da nadin shi ya ci gaba da zama a kujerar babban maishari...