fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Dangote Katsina

Gidauniyar Dangote ta bada tallafin kayayyaki ga ‘yan gudun hijira a jihar Katsina

Gidauniyar Dangote ta bada tallafin kayayyaki ga ‘yan gudun hijira a jihar Katsina

Tsaro
Gidauniyar Aliko Dangote (ADF) ta bayar da tallafin kayan agaji da kuma kudi Naira miliyan 5 ga dubunnan ‘yan gudun hijirar da ke cikin jihar Katsina don inganta jin dadin su. Kayayyakin wanda ya kunshi tabarma ta kwanciya guda dubu 10,000 , da kuma barguna mayafai dubu 10, da sauran kayayyaki, wanda gidauniyar ta baiwa gwamnatin jihar Katsina. Haka zalika gidauniyar ta bada kudi Naira Miliyan N5 ga Kungiyar Mata Musulmai ta Najeriya (FOMWAN) domin bayar da tallafi na musamman ga mata da yara dake Sansanonin 'yan gudun hijira dake a cikin Jiha. Idan zaku tuna jihar katsina na fuskantar barazana ga 'yan bindiga wanda suka addabi wasu kauyuka dake jihar Katsina ta hanyar kai hare hare tare da yin garkuwa da mutane.