
Dangote ya aike da sakon taya murna ga Dakta Ngozi
Shahrarran mai kudin Afurka Aliko Dangote ya aike da sakon taya murna ga Dakta Ngozi Okonjo Iweala bisa mukamin data samu na jagorantar kungiyar kasuwanci ta Duniya WTO.
Dangote ya aike da sakon ne ta shafinsa na sada zumunta dake Tuwita, inda ya yaba Da zabin da akiawa Dakta Ngozi tare da cewa lalle ya zama wajubi a yi Al'fahari da ita kasancewar ta mace ta farko data ajiye tarihi a matsayin shugabar kungiyar daga Afurka.