
Hotuna: Shugaban Majalisar Dattawa, Gwamnoni, Sakateren gwamnatin tarayya, Ministoci, da Sauransu Na Cikin Wadanda Suka Halarci Auren Senator Goje
Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Ahmad Lawan, gwamnoni biyu, Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha, wasu Sanatoci, da sauran manyan mutane sun halarci bikin auren sanata kuma tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Muhammad. Danjuma Goje, ranar Juma'a wanda ya aure Aminatu Dahiru Binani.
An gudanar da bikin ne a Asokoro, Abuja gidan ango.
Baya ga Shugaban Majalisar Dattawa da SGF, wadanda suka halarci gidan sanata Goje sun hada da Gwamna Muhammad Yahaya na jihar Gombe; Abdullahi Ganduje na jihar Kano; Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Dijital, Dr Isa Pantami; Sanata Gabriel Suswam, Abdullahi Adamu; da sabon Babban Daraktan Hukumar Kula da Gidaje ta Tarayya (FHA), Abdulmumin Jibrin.
Bikin ya kuma samu halartar tsoffin gwamnoni da na yanzu, ministoci, Sanatoci d...