fbpx
Thursday, May 19
Shadow

Tag: Dansanda

Dansandan Najeriya da yayi tatul da giya ya dirkawa wani mutum harsashi, ya Mutu

Dansandan Najeriya da yayi tatul da giya ya dirkawa wani mutum harsashi, ya Mutu

Tsaro
Wani sajan da ke aiki a ofishin ‘yan sanda na Elelenwo na rundunar‘ yan sanda reshen jihar Ribas ya harbe wani mutum mai suna Abiodun Jimoh mai shekaru 38 a harabar ofishin ‘yan sanda. An gano cewa sajan din, wanda ya bugu ne, ya kashe Jimoh a yayin takaddama kan takardun babur. A cewar jaridar Vanguard, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Ribas, Joseph Mukan, ya ce kisan harbin da aka yi wa“ ba tare da hujja ba ”da sajan din yayi kuma an kama shi kuma za a gurfanar da shi a gaban kuliya. Jimoh da kanen sa, Ismaheed, a yayin da suke tuka babur, sajan din wanda ‘yan sanda har yanzu ba su bayyana sunan sa ba, sun cafke su ne yayin wani sintiri da suka yi a yankin a ranar Juma’ar. Ismaheed, mai gyaran waya da laptop, wanda, tare da dan uwan ​​nasa, dan asalin jihar Kwa...
Hotuna: An kai matashin da ya mari dansandan Najeriya sau 2 kotu

Hotuna: An kai matashin da ya mari dansandan Najeriya sau 2 kotu

Tsaro
Hukumar 'yansandan jihar Legas sun sanar da kai wani matashi da ya faffallawa dansanda mari har sau 3 kotu.   Mutumun wanda hukumar 'yansandan bata bayyana sunan sa ba an kuma zargeshi da yiwa dansandan Barazana bayan ya haddasa Hadari.   Hukumar 'yansandan ta Alausa dake Legas data gurfanar da matashin yaki amsa laifinsa inda daga baya dai an nemi a tsareshi a gidan yari har zuwa 20 ga watan Janairu 2020 dan ci gaba da shari'ar. Police in Lagos say they have charged a man to court for allegedly slapping a policeman twice along Governor’s Road, Alausa, Ikeja, Igbere TV reports. The man whose identity was not revealed was also accused of threatening a police team on December 6 after causing an accident. According to an update by the police on Tuesd...
Yan Bindiga sun kai hari gidan tsohon gwamnan Bayelsa da kuma kashe dansanda

Yan Bindiga sun kai hari gidan tsohon gwamnan Bayelsa da kuma kashe dansanda

Uncategorized
Yan Bindiga sun kai Hari gidan tsohon gwamnan Bayelsa, Seriake Dickson inda suka harbi dansandan dake gadin gidan.   Lamarin ya farune a Toru-Orua dake karamar hukumar Sagbama a jihar. Yan Bindigar sun kai harinne da safiyar yau inda suka biyo ta ruwa.   Kakakin tsohon gwamnan, Fidelis Soriwei ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma mutuwar dansandan. Kakakin 'yansandan jihar, Asinim Butswat ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za'a fitar da sanarwa kan faruwar lamarin.
Inda Ranka:Yanda Zakara ya kashe dansanda

Inda Ranka:Yanda Zakara ya kashe dansanda

Siyasa
Wani dansanda da yaje kame a wani wasan da ake yi da zakaru a kasar Philippines ya rasa ransa sanadiyyar harin da zakaran ya kai masa.   Reza dake jikin kafar zakaran ta yanki dansandan a Cinya wanda hakan yayi sanadiyyar zubar da jini sosai, ko da aka kaishi Asibiti likitoci sun tabbatar da cewa ya mutu. Wasa da zakara Al'adace a kasar Philippines wadda aka yadda ayi ta a lokutan hutu da kuma da Ranekun da babu aiki. Saidai dalilin zuwan cutar Coronavirus/COVID-19,  Mahukunta a kasar Philippines sun haramta wasan.   Kamfanin dillancin labaran kasar PNA ya bayyana cewa lamarin ya farune a yankin Northern Samar.   Kamfanin Dillancin Labaran AFP ya ruwaito shugaban 'yansanda na cewa shekarunsa 25 yana aiki amma bai taba samun irin wannan Rahoto ba. Yac...
Dansanda ya kashe abokin aikinsa shima ya kashe kansa a Abuja

Dansanda ya kashe abokin aikinsa shima ya kashe kansa a Abuja

Siyasa
Wasu 'yansanda 2 a Abuja sun yi kace na ce akan zanga-zangar SARS a Mabushi. Lamarin yayi zafi sosai ta yanda daga karshe dayan ya dirkawa abokin aikin nasa harsashi.   Wani shaida yace suna cikin muhawara akan zanga-zangar SARS din kawai sai suka ji harbin bindiga, wanda aka harba din ya rika cewa, shikenan ya kasheni, daga baya kuma sai yayi addu'a ya mutu.   Abokan aikinsu dake kusa sun karasa wajan amma kamin su yi wani Abu tuni shima wanda yayi harbi  ya kashe kansa.   An dauke gawarsu aka tafi da ita kamar yanda Daily Trust  ta ruwaito.   “The two officers were arguing about the #EndSARS protest then we heard the sound of a gunshot. The other officer that was gunned down could be heard saying. ‘He has killed me,’ then he muttered some praye...
Dansanda, Rabiu Garba da ya gina fanfo da kudinsa na shan Yabo wajan ‘ya  Kudu, sun ce bai taba karabar Cin hanci ba

Dansanda, Rabiu Garba da ya gina fanfo da kudinsa na shan Yabo wajan ‘ya Kudu, sun ce bai taba karabar Cin hanci ba

Siyasa
Wani dansandan Najeriya, CSP Rabiu Garba wanda ke aiki a Fegge, Onitsha, Jihar Anambra nata shan Yabo a wajan 'yan jihar inda suka ce da kudinsa ya gina fanfan tuka-tuka.   Sun kuma bayyana cewa, yana shirya gasar kwallo tsakanin Matasa sannan kuma duk inda aka gayyaceshi koda cocine kuwa yana halarta.   Matasa sun je ofishin da yake aiki dan konashi kamar yanda ya faru a gurare da dama,  suna zuwa sai sauran 'yansandan suka tsere amma Rabiu bai tsere ba, koda ya fito, matasan suka ganshi sai suka fasa aniyarsu inda kuma ya musu hudubar cewa abinda suke yi ba me kyau bane. A good Cop: CSP Rabiu Garba, DPO, Fegge Police station Onitsha. Yesterday some youths in Onitsha mobilized to burn down some Police stations based on allegations of extortions and highhand...
Bidiyo: A aikin dansanda Da a kashe mara laifi 1 gara a bar dan fashi ya gudu>>Jami’in dansanda

Bidiyo: A aikin dansanda Da a kashe mara laifi 1 gara a bar dan fashi ya gudu>>Jami’in dansanda

Tsaro
Wani jami'in dansanda na ci gaba da shan yabo bayan da aka ga Bidiyonsa yana bayanin cewa da a kashe mutum mara laifi 1 gara a bar dan fashi ya gudu.   Dansandan wanda ba kai ga tantance ko wanene ba ya bayyana cewa abinda aka koya musu kenan a makarantar Horas da 'yansanda.   Yace yasan da yawa suna jin kunyar su saka kayan aiki a yanzu su fita. https://twitter.com/horlarwalebanks/status/1317428234577993729?s=19     Maganar tasa ta dauki hankula musamman saboda yanda a yanzu ake zanga-zangar SARS dakw nuna kyama ga miyagun 'yansanda.
SARS: Bidiyon yanda masu zanga-zanga a Delta suka kashe Dansandan Najeriya suka dauke Bindigar sa

SARS: Bidiyon yanda masu zanga-zanga a Delta suka kashe Dansandan Najeriya suka dauke Bindigar sa

Tsaro
A jiya, Alhamis ne aka samu Rahoton cewa an yi arangama tsakanin masu zanga-zangar ganin an kawo karshen rundunar 'yansanda ta SARS a Ughelli jihar Delta da 'yansanda.   Masu zanga-zangar wun budewa wasu 'yansanda wuta kamar yanda Rahoton yazo inda suka kashe daya suka dauke bindigarsa yayin da sauran abokan aikinsa suka tsere.   A sanarwar da hukumar 'yansandan ta fitar ta bayyana cewa, tana Allah wadai da lamarin kuma ba zata lamunci irin haka ba nan gaba, tace zanga-zanga hanya ce ga kowane dan kasa zai iya bayyana rashin jin dadinsa amma ba za'a basu wasu su rika fakewa da hakan suna aikata Laifi ba.   Shugaban 'yansandan ya aikewa da iyalan dansandan me suna, Etaga Stanley da ta'aziyyarsa inda yayi alkawarin kamo wanda suka yi wannan aika-aika dan huku...
Bidiyon yanda dansandan Najeriya ya tsere bayan ya dirkawa budurwarsa harsashi a baki

Bidiyon yanda dansandan Najeriya ya tsere bayan ya dirkawa budurwarsa harsashi a baki

Uncategorized
Wani dansandan Najeriya da ba'a kai ga tantancesgi ba ya tsere bayan dirkawa Budurwarsa harsashi a baki.   Lamarin ya farune a Salvation Bus Stop dake Ikeja birnin Legas. Bayan wannan aika-aika, dansandan ya tsere. Bidiyon lamarin da yayi ta yawo a shafukan sada zumunta ya dauki hankula sosai inda aka ga wasu bayin Allah sun dauki matar zuwa Asibiti.   An ga matar zaune dirshan a kasa a Asibiti tana fama da radadin harbin da ya lalata mata baki. Da Punch ta tuntubi kakakin 'yansandan jihar, Muyiwa Adejobi ya bayyana cewa, an gano dansandan da yayi wannan aiki amma ba a Rundunar 'yansandan Legas din yake ba.   Yace Budurwarsa ce kuma wani abune ya hadasu shi yasa ya harbeta amma zasu zakuloshi. Ya kara da cewa an aika 'yansanda Asibitin da aka kwantar...