fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Tag: Danyen Mai

Farashin danyen mai ya tashi zuwa Dala 40 a kasuwannin Duniya

Farashin danyen mai ya tashi zuwa Dala 40 a kasuwannin Duniya

Siyasa
Rahotanni sun bayyana cewa, Farashin Danyen Mai ya tashi zuwa Dala 40 a kasuwannin Duniya.   Farashin ya samu tagomashin kaso 2 cikin 100 ne wanda aka sayar da Brent akan Dala 40.53, kamar yanda Reuters ta tabbatar. Ana tsammanin rashin kyawun yanayi na kasar Amurka da ya hana kasar ayyukan hakar manta yanda ya kamata ne yasa farashin ya tashi sama.   Saidai masana sun bayyana cewa bukatar man zata ci gaba da raguwa saboda har yanzu kasashe basu kammala farfadowa daga matsin tattalin arzikin da Annobar cutar Coronavirus/COVID-19 ta zo dashi ba.
Tonon Solili: Yanda jami’an Gwamnatin tarayya dana NNPC suka sayar da Gangar mai Miliyan 48 da aka sata sannan suka yiwa wanda ya tona lamarin barazanar kisa

Tonon Solili: Yanda jami’an Gwamnatin tarayya dana NNPC suka sayar da Gangar mai Miliyan 48 da aka sata sannan suka yiwa wanda ya tona lamarin barazanar kisa

Siyasa
A shekarar farko ta shugaban kasa,Muhammadu Buhari akan mulki, 2015 an saci danyen mai ganga miliyan 48 daga Najeriya.   An kai wannan danyen mai kasar China inda aka yi yunkurin saidashi, saidai daya daga cikin kamfanoni da aka tuntuba dan ya sayi man, SAMANO SA DE ya fahimci cewa man na satane. Dan haka ya kwarmatawa gwamnatin Najeriya da lamarin inda ya aikewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari da wasika. Saidai wasu na kusa da shugaban kasar sun hana wasikar kaiwa ga shugaban kasar inda suka karkatar daman daga kasar China zuwa wani guri inda aka sayar da man  ba tare da sanin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba kuma kudin da aka sayar din ba'a sakasu a lalitar gwamnati ba.   Da wannan kamfani ya nemi a bashi kasonshi da doka ta tanada ga duk wanda ya kwarmata ...
Farashin gangar mai ta kara faduwa zuwa dala 15

Farashin gangar mai ta kara faduwa zuwa dala 15

Kasuwanci
Rahotanni sun bayyana cewa, farashin gangar danyen mai na Brent wanda da shine akewa man Najeriya farashi ya kara faduwa zuwa Dala 15.98 kamar yanda Reuters ta ruwaito.   Wannan shine farashi mafi karanci da man ya taba kaiwa tun shekarar 1999, kusan shekaru 21 kenan.   Rahoton yace man ya dan farfado inda aka rika sayar dashi akan Dala 16.63.   Rahoton ya kara da cewa farashin man ya fadi da kashi 80 cikin 100 a shekararnan saboda Annobar cutar Coronavirus/COVID-19 data mamaye Duniya kuma ta yi sanadin mutuwar mutane kusan 180,000.   Yawan man da ake kaiwa kasuwar Duniyar ya zarce bukatar man da ake dashi, sannan kasar da ta fi kowace yawan samar da kaya,Amurka na faman neman inda zata ajiye rarar man da take dashi.   Man Amurka dai y...
Farashin danyen Mai a kasuwar Duniya ya kara faduwa zuwa Dala 19

Farashin danyen Mai a kasuwar Duniya ya kara faduwa zuwa Dala 19

Kasuwanci
Rahotanni sun bayyana cewa farashin gangar danyen mai na Duniya da ake kira da Brent ya kara faduwa kasa inda ya koma Dala 19.   Akan farashin Brent ne ake sayar da dayen man Najeriya.   Farashin danyen man na ci gana da faduwa kasa duk da rage yawan danyan man da kasashe kungiyar OPEC sukayi. Hakan baya rasa nasaba da rashin bukatar sayen man daga kasashen da yawanci suke kulle saboda dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19.   Najeriya dai ta rage farashin danyen man data yi kasafin kudinta akai daga Dala 57 zuwa dala 30.   Kasar Saudiyya ta bayyana cewa tana kallon yanda farashin man ke gudana kuma zata dauki mataki.