fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Darika

Kungiyoyin Agaji Na Shi’a, Izala Da Darika Sun Yi Aikin Gyaran Asibiti Tare A Garin Bakori

Kungiyoyin Agaji Na Shi’a, Izala Da Darika Sun Yi Aikin Gyaran Asibiti Tare A Garin Bakori

Siyasa
A ranar Lahadi 28/06/2020 wasu gamayyar kungoyoyin bada agaji da taimako da suka hada da Harisawa daga bangaren Shi'a da Kungiyar bada Agaji ta Izala da kuma 'Darika suka hadu waje guda inda suka gudanar da gagarumin aikin gayya domin tsaftace da gyara babban Asibiti garin Bakori dake Jihar Katsina gami da temaka marassa lafiya da abubuwa da dama. Yayin aikin an share dukkan haraban asibitin sannan aka hada da ciki wajan kwantar da masu jinya. An wanke dukkan ciki da waje da amfani da sabulun kashe cutuka, an gyara wasu abubuwan da suka lalace. An cire dukkan datti hatta a makwantan masu jinya. An hada hatta bayikan zagawa sannan aka yi feshin maganin cutuka da kuma kwari, daga karshe aka dauki hotuna aka watse. Rariya.
Rikicin limanci tsakanin izala da darika ya jikkata mutum takwas

Rikicin limanci tsakanin izala da darika ya jikkata mutum takwas

Uncategorized
Rikicin limanci a babban masalacin juma’a na garin Okene a tsakanin ‘ya’yan kungiyar Izalatul bidi’a wa’ikamatus sunnah da na ‘yan darikar Tijjaniya ya jikkata mutum takwas a jihar Kogi.     Majiyar Aminiya ta shaida cewa tun bayan rasuwar babban limamin masalacin, Shaikh Musa Galadima a shakarar 2019,  ake samun tashin tashana a tsakanin kungiyoyin biyu akan wanda zai gaji marigayin,  ya ci gaba da bada sallah a matsayin sa na babban limami a masallacin.     Wasu da suka shaida faruwar Lamarin sun shaida wa Aminiya cewa, rikicin da ya faru a ranar juma’a, 15 ga watan Mayu ba shi ne irin sa na farko ba a masallacin domin a baya ma an taba kwata irin  hakan a tsakanin kugiyoyin Islama biyu masu banbancin ra’ayi inda ko wane bangare ke fatan jan raga...