fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: Daso

Daso na neman wata Masoyiyarta da ta yi ankon kaya da ita

Daso na neman wata Masoyiyarta da ta yi ankon kaya da ita

Nishaɗi
Wata masoyiyar tauraruwar fina-finan Hausa, Saratu Gidado da aka fi sani da Daso ta yi ankon kaya da ita ta saka a shafinta na sada zumunta.   Ta yiwa hoton taken soyayyar da nakewa Mama Daso.   Hankalin Dason ya kai kan Hoton inda ta bayyana jin dadinta tare da kira ga duk wanda yasan wannan baiwar Allah to yace ta aika mata da sakon karta kwana. Dan ta yi mata kyauta. https://www.instagram.com/p/CFeR2Q-h2QM/?igshid=18xjctls1do1k Daso dai ta bayyana cewa ta kasa Gano ta a Facebook.   Saidai Binciken Hutudole ya gano shafin baiwar Allahn me sun Phaty Abdallah kamar haka: https://www.facebook.com/phaty.abdallah   Amma a iya Binciken mu ba mu ga wannan Post din da ta yi akan Daso ba.  
Fyade: Daso ta baiwa Iyaye shawarar da idan suka bi zasu kiyaye ‘ya’yansu

Fyade: Daso ta baiwa Iyaye shawarar da idan suka bi zasu kiyaye ‘ya’yansu

Nishaɗi
Tauraruwar fina-finan Hausa,Saratu Gidado da aka fi sani da Daso a karo na 3 ta sake sakin Bidiyo inda a ciki take jan hankalin iyaye dasu rika kula da 'ya'yansu dan sakacin wasu iyayen na kaiwa ga a yiwa 'ya'yansu fyade.   Daso ta saka sakonnate a shafinta na Instagram inda ta bayyana cewa idan baka samarwa 'yarka abinda zata sayi alewa ba idan wani ya ganta a waje ya bata zata iya binshi. Daso tace a koyawa yara idan wani ya tanasu su cijeshi su kuma yi ihu. https://www.instagram.com/tv/CBVWekmgPX5/?igshid=3noyt5r97kmi A baya dai Daso ta sako bidiyo 3 akan wanan lamari, kamar yanda muka kawo muku inda a cikin daya daga cikinsu take cewa Allah ya tsinewa masu fyaden idan ba masu shiryuwa bane.