fbpx
Friday, December 2
Shadow

Tag: Dauda Kahutu(Rarara)

Tunda Muka taso muke jin ana cewa Buhari me gaskiya, Kun kara jin ana cewa wani me gaskiya Duk Najeriya?>>Rarara

Tunda Muka taso muke jin ana cewa Buhari me gaskiya, Kun kara jin ana cewa wani me gaskiya Duk Najeriya?>>Rarara

Siyasa
Tauraron mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa tun suna kananan yara ake cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari me gaskiya kuma har yanzu ana fada.   Rarara ya bayyana hakane a hira ta musamman da Kannywood exclusive suka yi dashi kan akan sabuwar wakar da zaiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari wadda yace talakawane zasu biya kudin yin wakar. Rarara yace yana da niyyar tattaro duka ayyukan da shugaban kasar yayi daga kudu da Arewa dan bayyanasu a cikin wakar tasa, saboda wasu basu san dasu ba.   Da yake magana akan Nagartar shugaban kasar, Rarara yace tunda suna yara ake cewa shugaba Buhari mai Gaskiya kuma har yanzu ana fada. https://m.youtube.com/watch?v=juH3PYSb6IU Ya tambayi wadda ke masa tambayoyi cewa shin duk Najeriya ta kara ji ance ga ...
Tun muna yara ake ce mana Buhari me gaskiyane:Bashi da laifi a gurin mu>>Rarara

Tun muna yara ake ce mana Buhari me gaskiyane:Bashi da laifi a gurin mu>>Rarara

Siyasa
Tauraron mawakin Siyasa wanda ya kware wajan yiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari wakar Yabo, Dauka Kahutu Rarara ya bayyana cewa su a gurinsu Shugaban kasar bashi da laifi.   Ya bayyana hakane a wata tattaunawa ta musamman da Kannywood exclusive suka yi dashi inda aka tambayeshi cewa 'yan Najeriya basu taba jin ya fadi laifin shugaban kasa ba. Sai ya kada baki yace ai su a gurinsu shugaba Buhari bashi da laifi. Yace indai a cikin sauaran 'yan siyasa ne musamman wanda suka gabata to shugana Buhari ba zai yi laifi ba.   Yace bece shugaban kasar ma'asumi bane amma idan za'a kwatantashi da sauran 'yan siyasa to za'a ga bashi da laifi.   Da aka masa maganar tsadar Rayuwa, Rarara yace wannan duk Duniya ne kowace kasa ta tabu yace a lokacin da APC ta zo ta...
Dan Allah ka sammin Miliyan 2 daga cikin kudin da ‘yan Najeriya suka tara maka>>Wani Ya roki Rarara

Dan Allah ka sammin Miliyan 2 daga cikin kudin da ‘yan Najeriya suka tara maka>>Wani Ya roki Rarara

Siyasa
Wani bawan Allah me suna Mallam Nuhu wanda daya daga cikin mabiyan shafin hutudole ne ya nemi taimakon tauraron mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara.   Yace yana rokon Rarara ya taimaka masa da Naira Miliyan 2 daga cikin kudaden da 'yan Najeriya suka tara masa yawa shugaba Buhari waka. Ya bayyana lambar wayarsa da 08068004606, Sai Asusun Ajiyar kudinsa na banki: 0056355810 Yace shi dan jihar Adamawane.   Akwaidai wasu rahotanni dake cewa Rarara ya samu kudin da suka haura Miliyan 70.
Idan Na fidar da wakar Buhari ‘yan Adawa sai sun rasa bakin Magana>>Rarara

Idan Na fidar da wakar Buhari ‘yan Adawa sai sun rasa bakin Magana>>Rarara

Nishaɗi
Tauraron mawakin Siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa idan ya fitar da wakar da yake shirin rerawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari to 'yan Adawa Gum zasu yi.   Yayi wannan bayanine a karin hasken da yayi kan tara masa kudin Dubu-Dubu da zaiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari waka dasu. Yace a daina biyewa 'yan Jarida suna wallafa kanun Labarai masu daukar hankula ne kawai amma shi yana so ne ya nunawa 'yan Adawa cewa har yanzu akwai masoya shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma suma tare dashi hakanan shima yana tare dasu.   Rarara yace idan fa ya saki wannan waka tashi to ko 'yan Adawa dole su saki kari dan ba zasu ce ba'a musu komai ba. Yace zai zayyano ayyukan da shugaban kasar yayi ne a wakar tasa.
Bidiyo:Biliyan 2 Rarara ke son tarawa daga hannun masoya shugaban kasa kamin ya fara waka

Bidiyo:Biliyan 2 Rarara ke son tarawa daga hannun masoya shugaban kasa kamin ya fara waka

Siyasa
Tun bayan da Tauraron mawakin Siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana neman tallafin Naira Dubu-Dubu daga hannun masoya shugaban kasa, Muhammadu Buhari da yiwa shugaban kasar waka, hankula suka koma kan wannan lamari sosai.   Ya zuwa yanzu dai masoyan shugaban kasar da dama nata turawa Rarara tarin kudi da dama dan ya rerawa gwanin nasu waka.   A wani Rahoto da Kannywood exclusive ta ruwaito tace wata majiya ta gaya mata cewa Biliyan 2 Rarara ke son tarawa daga masoyan shugaban kasar kamin ya fara waka. Saidai zuwa yanzu babu rahoto kan nawa mawakin ya tara. https://m.youtube.com/watch?v=oCed5R5XwCE
‘Yan Kasuwar Kantin Kwari Dake Kano Suna Cigaba da Tattara Makudan Kudaden da Za Su Turawa Mawaki Rarara

‘Yan Kasuwar Kantin Kwari Dake Kano Suna Cigaba da Tattara Makudan Kudaden da Za Su Turawa Mawaki Rarara

Siyasa, Uncategorized
Kungiyar 'yan kasuwar Kantin Kwari dake Kano sun dauki aniyar tarawa fitataccen mawaki Dauda Kahutu Rarara makudan kudade domin ya yi wa Shugaban kasa Muhammad Buhari waka.   'Yan Kasuwar sun kudiri aniyar tattara kudaden guri guda a dunkule, inda kowa zai bayar da tasa gudunmawar ta naira dubu daya. Wanda daga karshe za a tura su a cikin asusun ajiyar banki na Mawakin. Idan ba a manta ba, Rarara ya bukaci masoya Buhari da su tura masa naira dubu dai-dai kafin ya yi wakar.
Rarara me kudi ne kawai dai yana so ya nunawa Duniya cewa har yanzu akwai Miliyoyin ‘yan Najeriya masoya Shugaba Buhari>>Ahlan

Rarara me kudi ne kawai dai yana so ya nunawa Duniya cewa har yanzu akwai Miliyoyin ‘yan Najeriya masoya Shugaba Buhari>>Ahlan

Siyasa
Tsohon tauraron fina-finan Hausa, Sharif Ahlan ya kare tauraron mawakin Siyasa, Dauda KahutubRarara kan wakar da yace zaiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda ya nemi masoyan shuga an kasar da su tara kudi Dubu-Dubu dan yahi wakar. Ahlan ya bayyana cewa matsalar mutanenmu shine akwai hassada da ganin kashi. Yace Rarara baicewa kowa ya tura masa kudi ba, yace ne masoyan shugaban kasa, Muhammadu Buhari yake magana, yace kuma wannan waka bai ma riga yayi ta ba amma ana ta caccakarsa, wanda hakan yake nuna masu sukar nasa mutanene masu gajeren Tunani.   Yace ai a bari ya saki wakar tukuna a ji abinda zai fada kamin a fara sukarsa. Ahlan yace kamar yansa yakewa 'yan siyasa Rubuce-rubuce a jaridun turanci yana koresu to haka zaiwa Rarara shima ya gayawa Duniya Muhimmancinsa. ...
Amma Rarara ya rainawa Talakawa wayau, da wanne zasu ji?>>Hakeem Baba Ahmad

Amma Rarara ya rainawa Talakawa wayau, da wanne zasu ji?>>Hakeem Baba Ahmad

Uncategorized
Dan siyasa kuma Me fada Aji a jihar Kaduna, Hakeem Baba Ahmad yayi martani akan neman da mawakin shugaban kasa, Muhammadu Buhari,  watau Dauda Kahutu, Rarara yayi na a tara masa Dubu-Dubu yayi waka.   A wani Rubutu da yayi a shafinsa na Faceboon, Hakeem ya bayyana cewa rara ya rainawa Talakawa wayau inda yace a halin matsin da ake ciki shin da wanne zasu ji?   Ga dai cikakken abinda ya rubuta:   "Kai jamaa, amma gaskiya Rarara ya raina wa talaka wayau.Wai duk kudin da yayi ta samu sanadin Shugaba Buhari, yanzu sai talakawan da ke cikin mummmunan matsi, kuma masu son Buhari sun biya shi Naira dubu-dubu sannan ya rera masu sabon wakar yabon Buhari.Idan kuma basu biya ba, ba zai yabi Buharin ba ke nan. A karshe dai kila wata dabara ce kawai ya shirya ta kara ...
Hotuna:Masoyan Buhari na tururuwar Turawa Rarara Dubu 1

Hotuna:Masoyan Buhari na tururuwar Turawa Rarara Dubu 1

Siyasa
Ga dukkan Alamu ba kamar yanda wasu musamman 'yan hamayya da wanda suka sauka daga motar goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari ke tsammani ba, har yanzu akwai 'yan gani kashenin shugaban kasar. A jiyaje shahararren mawakin shugaban kasar, Dauda Kahutu, Rarara ya bayyana cewa yana neman masoya shugaban kasar su tara masa kudi ta hanyar aika Naira Dubu 1 kowannensu.   Wannan bukata ta Rarara ta tada kura inda wasu ke cewa sam ba zasu iya ba, wasu kuwa na cewa ko nawane zasu tura, kai wani ma ya bayyana cewa ko dubu 50 ne zai tura.   Saidai yayin da wasu ke fada da baki, wasun kuwa tuni suka fara turawa Rarara wannan kudi inda suka saka hotunan shaidar hakan kamar yanda za'a iya gani a kasa.
Rarara ya daina rerawa Buhari waka

Rarara ya daina rerawa Buhari waka

Siyasa
Fitaccen mawakin 'yan siyasar nan da masu mulki a Najeriya wato Dauda Kahutu Rarara, yace daga yanzu ya daina yiwa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari waka, har sai masoyan shugaban kasar sun biyashi kudin rera wakar. A zantawar sa da wakilin RFI Hausa Abuabakar Isah Dandago, Rarara, yace irin cece kucen da ya karade kafafen sada zumunta kan cewar shugaba Buharin ya gaza ya sanya shi soma shelar neman masoyan shugaban na zahiri da suka kada masa kuri’a su yi karo karon naira dubu guda guda matsawar sunason ya dawo fagen cigaba da yiwa Buharin waka, idan kuwa bahaka ba shikam bazai kara yiwa shugaban waka ba.   Rarara wanda ya yi suna wajen yada manufar shugaban Najeriyar ta hanyar wakokin sa, yace a tasa fahimtar wadanda ke sukar shugaba Buhari ba sune suka kada masa kuri’...