
Rarara na neman karo-karo na Dubu 1 daga hannun talakawa dan yiwa shugaba Buhari waka ta musamman
Fittacen mawakin siyasa Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara, yace zai je har fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin neman yafiyar sa akan ba ta masa suna da makiyan sa keyi ta shafukan sada zumunta da sauran kafafen watsa labarai, kuma zai je wajen shugaban ne a madadin talakawan Nijeriya.
Rarara ya ce, gwamnatin APC na kokari matukar gaske, wajen ganin ta samar da cigaba, saidai kuma cutar korona bairos ta kawo mata cikas, kuma zai yi waka mai suna ‘’Kainuwa" wacce zai bayyano ayyukan shugaban kasa guda 192, kuma talakawan Nijeriya ne za su dauki nauyin wakar, saboda haka kowa yana iya bada nasa tallafin daga kan N1,000 zuwa sama, ta hanyar tura masa a asusun ajiyarsa na banki.
‘’Zan nemi ganin shugaban kasa, na ce masa, talakawa suna kara baka hakuri da wan...