fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Tag: Daura

Shugaba Buhari ya koma Abuja bayan hutun kwana 4 a Daura

Shugaba Buhari ya koma Abuja bayan hutun kwana 4 a Daura

Uncategorized
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya koma fadarsa dake babban birnin tarayya, Abuja bayan hutun kwanaki 4 a mahaifarsa dake Daura.   Shugaban ya koma Abuja da yammacin yau, Talata ne, kamar yanda hadiminsa, Bashir Ahmad ya bayyana ta shafinsa na sada zumunta.   Shugaba Buhari ya je daura inda ya sabunta rijistarsa ta APC. https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1356660293364023302?s=19 President @MBuhari has returned to Abuja this evening, after a four-day official visit to his hometown, Daura, Katsina State.
Gamayyar Kungiyoyin Arewa zasu yi tattaki zuwa Daura dan yiwa shugaba Buhari zanga-zangar satar daliban da aka yi

Gamayyar Kungiyoyin Arewa zasu yi tattaki zuwa Daura dan yiwa shugaba Buhari zanga-zangar satar daliban da aka yi

Uncategorized
Hadaddiyar kungiyar yan Arewa ta ce shugabannin kungiyar na jihar za su yi tattaki zuwa garin Daura, mahaifar shugaban kasar, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), don nuna adawa da sace akalla daliban makarantar sakandaren Gwamnati ta 333, Kankara, Jihar Katsina. A karkashin tutar kamfen din #Bringbackourboys, mai magana da yawun CNG, Abdul-Azeez Suleiman, ya fadawa manema labarai a ranar Litinin cewa mambobin sa za su afka gidan shugaban a yau kuma su ci gaba da zama har sai an ceto daliban 333 da suka bata. Ya ce, “Su ma shugabanninmu na jiharmu suna kan yin wata tafiya mai nisa zuwa Daura don neman daukar matakin gaggawa daga Buhari wanda yake Daura a halin yanzu. “Kungiyar CNG ta Kano za ta tashi daga Dambatta don hadin kai da reshen Katsina don hadewa da tawagar Jig...
Bidiyo Yanda aka gudanar da zagayen Maulidi a Daura

Bidiyo Yanda aka gudanar da zagayen Maulidi a Daura

Siyasa, Uncategorized
An Gudanar Da Zagayen Babban Maulidi A Daura ranar sabar Asabar.   Ranar Asabar,28 ga watan Nuwamba ne Mabiya Darkara Tijjaniya Suka Gabatar Da Babban Maulidin Zagaye Wanda Akeyi A Duk Shekara Domin Tunawa Da Ranar Haihuwan Manzo Allah S.A.W.   Maulidin Zagaye Na Garin Daura Yana Daukar Hankali Sosai,Domin Ana zuwa Daga Wasu Jahohi Daban-Daban Domin yin Maulidin, Wanda Yan'Shia Ma Sunayin Nasu A wajen. Kuma Ana Kai Kimamin Hour 2 Anayi. https://youtu.be/CH2inwjVTHU Wanda Aka Gudanar Da Maulidin Da Manyan Malamai kamarsu Sheikh Dahiru Usman Bauchi Da Sauransu.
Kyauta kamfanin China zai gina jami’ar Sufuri ta Daura>>Amaechi

Kyauta kamfanin China zai gina jami’ar Sufuri ta Daura>>Amaechi

Siyasa
Ministan Sufurin,  Rotimi Amaechi ya bayyana cewa a kyauta kamfanin kasar China na CCECC zai gin jami'ar Sufuri ta Daura.   Ya bayyana hakane yayin da yaje ran gadin aikin a Daura inda yace alkawarin da aka yi shine 'yan Chinar zasu kwashe shekaru 5 suna aiki a makarantar inda daga nanne kuma sai Najeriya ta karba. Yace ana tsammanin shafe shekara 1 ana ginin Jami'ar kuma akwai makarantun sakandare dana Firame da za'a gina a cikin jami'ar saboda ma'aikatan da zasu je daga nesa.   Jami'ar dai za'a gina ta ne akan kudi Dalar Amurka Miliyan 50. Hutudole ya samo muku cewa 'yan Najeriya da dama sun nun rashin jin dadinsu akan hakan inda suke cewa ya kamata a bincika dai kasar China ba zata yi komai a kyauta ba, akwai wani abu a kasa.
Za’a kammala ginin jami’ar Sufuri ta Daura nan da watan Satumba na 2021>>Amaechi

Za’a kammala ginin jami’ar Sufuri ta Daura nan da watan Satumba na 2021>>Amaechi

Uncategorized
Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa nan da watan Satumba na shekarar 2022 ne kamfanin kasar China na CCECC zai kammala aikin ginin Jami'ar Sufuri da za'a yi a Daura.   Ya bayyana hakane a yayin da yakai ziyara wajan ginin jami'ar a garin Daura dake jihar Katsina. Amaechi ya bayyana cewa, kamfanin ya samu amincewar gwamnatin jihar wajan ginin sannan kuma nan da watan Satumba zai fara ginin. Yace yana tsammanin nan da watan Satumba na shekarar 2021 za'a kammala ginin jami'ar.
Sarkin Daura ya sake fasalin majalisar hakimansa

Sarkin Daura ya sake fasalin majalisar hakimansa

Siyasa
Mai martaba Sarkin Daura, Dr. Umar Farouk, ya kawo sauyi ga wasu yan Majalisun sa don inganta zaman lafiya da hadin kai a masarautar. Babban jami’in yada labarai na majalisar masarautar, Muhammad Ibrahim ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar laraba a fadar sarki da ke Daura. Ibrahim ya ce sarkin tsafta na Daura, Alhaji Lawal Usman, an mayarda shi a matsayin sabon Kauran Daura, wanda ya sanya shi (Usman) ya kasance cikin masu zaban sarki na masarautar Daura, yayin da Sarkin Sudan, Alhaji Yusuf Nalado, zai yi aiki a matsayin babban jami'i na musamman mai ba da shawara ga mai martaba sarki. A cewar kakakin, mai magana da yawun sarkin ya ce, sabbin majalisun da aka gabatar da su don su yi aiki da aminci da adalci tare da inganta zaman lafiya ...
Mun gode Allah Sarkin Daura ya samu lafiya>>Buhari

Mun gode Allah Sarkin Daura ya samu lafiya>>Buhari

Uncategorized
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce yana cike da farin cikin bisa samun lafiya da Sarkin Daura, Umar Farouk ya yi.     A wani sakon da mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shugaba Buhari ya ce " ina farin cikin sallamar da aka yi maka daga asibiti bayan samun lafiya musamman a wannan zamani na annoba da hankali ke tashi idan mutum ba shi da lafiya."     An dai kwantar da Sarkin Daura, Umaru Farouk a asibitin gwamnati da ke Katsina ranar Talata sakamakon larurar da ba a fayyace ba.     Wata majiya a fadar wadda ba ta son a ambaci sunanta ta shaida wa BBC cewa an fitar da Sarkin ne daga fadarsa da misalin karfe dayan dare na Talata inda aka garzaya da shi zuwa birnin Katsina.   &n...
Bidiyo: Sarkin Daura na kara samun sauki sosai

Bidiyo: Sarkin Daura na kara samun sauki sosai

Uncategorized
Me martaba Sarkin Daura, Umar Farook Ya bayyana a cikin wani Bidiyon daya watsu sosai a shafukan sada zumunta inda aka ganshi yana Murmurewa.   Sarkin Daura dai yayi fama da rashin Lafiya wadda ba'a bayyana kalarta ba a hukumance.   A sabon bidiyon daya bayyana, an ganshi a Asibiti, fadawa nata kwasar Gaisuwa kuma daga baya aka ga ya tashi ya koma ciki. Rahotanni sun bayyana cewa Asibitin gwamnatin tarayyane dake Katsina, muna fatan Allah ya karawa Sarki Lafiya.