
2023: Hotunan Wasu matasan Arewa suna nemi gwamnan Ebonyi ya tsaya takarar shugaban kasa
Wasu matasan Arewa sun nemi gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi ya tsayata takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023.
Matasan sun fito ne daga jihar Jigawa, kuma sun bayyana masa hakane ne yayin da ya kai ziyarar aiki jihar ta Jigawa.
Matasan sun fito da yawa dauke da kwalaye masu kira ga gwamnan da ya fito takara saboda sun gamsu da aikin raya kasa da yake a jiharsa. Hutudole ya fahimci cewa gwamnan ya je jihar ne dan kaddamar da aikin titin garin Babura wanda gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya gina.
A yayin kadadamar da tititunan, Gwamna Umahi ya bayyana cewa APC tana aiki amma ba'a yayatasu yanda ya kamata. Ya jinjinawa Gwamna Badaru bisa ayyukan raya kasa.
"We have served in various National assignments together and I have come to realiz...