Beckham yace Messi yafi Cristiano Ronaldo kuma shine zakaran wasan kwallon kafa na duniya
David Beckham ya bayyana ra'ayin shi gami da muhawarar da ake yi akan Cristiano Ronaldo da Lionel Messi. Tsohon tauraron Manchester United din yace zakaran Barcelona yafi tauraron Juventus kuma shine zakaran wasan kwallon kafa na duniya.
Beckham ya taka muhimmiyar rawa a wasan kwallon kafa yayin da yayi nasarar lashe gasar premier lig da champions lig da kuma la liga, kuma yayi nasarar juwa a na biyu a kyautar balloon d'Or na shekara ta 1999.
Becham yayi wasa a manyan kungiyoyi kamar irin su man United, Real Madrid, PSG, Ac Milan da LA Galaxy.
Beckham yace Messi shine babban dan wasa cikin yan wasan daya taba fuskanta a wasannin kwallon kafa, kuma ba abu mai yiwuwa bane ace za'a samu wani kwararren dan wasan kamar shi ba.
Messi a koda yaushe shine yake taimakawa Barcelona s...