
Da Dumi Dumi: Kungiyar daliban Najeriya (NANS) ta goyi bayan gwamnan Ebonyi, David Umahi daya cigaba da mulki
Kungiyar daliban Najeriya (NANS) ta marawa David Umahi da mataimakinsa Kelechi Igwe baya dasu cigaba da mulki duk da cewa babbar kotu ta kore su.
Babbar kotun Abuja ta kore gwamnan Ebonyi da mataimakinsa ne saboda sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Inda ta bayyana cewa kuri'ar datasa ya zama gwamna ta PDP ce, amma duk da haka kungiyar dalibai ta mara mai baya daya cigaba da mulkinsa inda tace abinda akayi mai ba adalci bane.