
Tsohon kaftin din Manchester City David Silva ya turawa masoyan City sakon bankwana bayan ya koma Real Sociedad
Kungiyar Lazio suna da tabbacin cewa Silva zai amince da bukatun su domin sunyi mai kwantirakin shekaru uku sannan zasu ringa biyan shi euros milyan 10 a kowace shekara, amma dan wasan ya zabi komawa Real Sociedad wanda suka kasance na shida a teburin Serie A na wannan kakar.
Dan wasan Sifaniyan ya bar kungiyar Manchester City bayan yayi shekaru goma a kungiyar kuma yayi nasarar lashe kofuna 11 a kasar Ingilan wanda suka hada da kofunan Premier League guda hudu.Silva ya shigo wasan quarter final da Lyon ta cire City 3-1 a gasar Champions League daga benci, kuma Man City ta sanar ranar litinin cewa zata yi mutun mutumi domin girmama Silva duk da ya bar kungiyar su saboda jajircewar shi.
David Silva ya turawa masoyan City sakon bankwana a shafin shi na Twitter ranar litinin, yayin da...