
Duk tsoron Allahn ka sai ka hada kai da miyagu kamin ka zama shugaban kasar Najeriya>>Tsohon dan takarar shugaban kasa, Dele Momodu
Tsohon dan takarar shugaban kasar Najeriya kuma me jaridar Ovation Magazine, Dele Momodu ya bayyana cewa ba zai sake tsayawa neman takarar shugabancin Najeriya ba.
Yace dalili kuwa shine ba zai iya yin abinda ake yi kamin a zama shugaban kasar Najeriya ba. Yace irin hanyar da ake bi kamin a samu shugabancin Najeriya shiyasa koda shugaban kasa na son yawa mutane aiki ba zai iya ba.
Yace duk tsoron Allahn ka sai ka hada kai da miyagun mutane kamin ka zama shugaban kasa a Najeriya. Yace to bayan ka zama shugaban kasar dolebe kuwa ka musu abinda suke so tunda sun taimakeka.
Ya bayyana cewa shi kuma gaskiya ba zai iya hada kai da miyagu ba saboda kawai yana so ya mulki Najeriya. Yace yana da kwarewar da zai iya mulkar Najeriya amma wannan daliline yasa shi ya h...