fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: Delta

Covid-19: Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta cafke mutane 46 Da suka karya dokar hana fita

Covid-19: Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta cafke mutane 46 Da suka karya dokar hana fita

Crime
Rundunar ‘yan sanda a jihar Delta ta cafke mutane 46 saboda karya dokar hana zirga-zirga da gwamnatin jihar ta sanya domin hana yaduwar cutar COVID-19. Wadanda ake zargin suna daga cikin mutane 98 da ake zargi da aikata laifi da ‘yan sanda suka kama a fadin jihar kan laifuka daban-daban da suka hada da fashi da makami, kungiyar asiri, sata da kuma fyade. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Mohammed Ali , wanda ya gabatar da wadanda ake zargin a ranar Asabar ya shawarci iyaye da su gargadi’ ya’yansu game da aikata laifi.
Yan bindiga sun kashe dan sandan, inda suka yi awon gaba da bindigar AK-47 a jihar Delta

Yan bindiga sun kashe dan sandan, inda suka yi awon gaba da bindigar AK-47 a jihar Delta

Tsaro
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da harbe wani dan sanda a jihar Delta. Jaridar DAILY POST ta tattaro cewa lamarin ya faru ne kusa da sabon yankin Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa na Najeriya, NPA a Warri. Maharan sun tafi da bindigarsa AK-47. An gano cewa mamacin yaje rakiyar abokin shi ne lokacin da 'yan bindigar suka kashe shi. Hutudole ya ruwaito muku cewa, Lokacin da aka tuntube shi don jin ta bakin, Jami’in Hulda da Jama’a na ’Yan sandan Jihar Delta, DSP Onome Onovwakpoyeya, ya tabbatar da rahoton a wani sakon tes. Sakon rubutu ya ce “Ee, kuma wannan labarin ne labarin kawai”.
‘Yan bindiga A jihar Dalta sun hallaka wasu Jami’an ‘yan sanda 3

‘Yan bindiga A jihar Dalta sun hallaka wasu Jami’an ‘yan sanda 3

Tsaro
Rahotanni na nuni da cewa a jiya ne wasu 'yan bindaga suka afkawa wasu jami'an 'yan sanda a jihar Delta wadanda ke kan aiki a daura da Otal din Ughelli inda sukai Nasarar kashe jami'ai uku tare da kwace musu bindigogin su. Wata Majiya ta bayyana cewa Jami'an da aka kashe Madaki Lawan da Ibrahim yau kusan shekara guda da yi musu canjin aiki zuwa Jihar Dalta daga Zarai. Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Onome Onovwakpoyeya ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a jihar.    
Wasu ‘yan bindiga a jihar Delta sun hallaka wani makanike mai gyaran janerata har Lahira

Wasu ‘yan bindiga a jihar Delta sun hallaka wani makanike mai gyaran janerata har Lahira

Crime
A ranar Talata ne rahotanni suka bayyana labarin wani Makanike dake gyaran Janerato wanda ke kan sana'arsa a dai-dai lokacin da wasu da ake kyautata zaton 'yan fashine suka hallaka shi har lahira. Lamarin dai ya faru ne a jihar Delta, wanda al'amarin ya rutsa da wani da ake kira da suna Kelvin Asaboro, hakanan 'rahotanni sun kuma shaida cewa, Yan bindigar sun kuma harbe wasu mutane hudu a yayin da suke kokarin aikata fashin da Makami. Wasu shaidaun gani da ido sun tabbatar da cewa, Tuni aka kwashe gawarwakin mamatan zuwa dakin ajiye gawawwaki, sai dai wasu fusatattun Matasa A yankin sun banka wa tayoyi wuta wanda ya haddasa toshewar hanyoyin wucewa a yankin. Shima Jami’in Hulda da Jama’a na ’Yan sanda na Jihar Delta, DSP Onome Onovwakpoyeya, ya tabbatar da rahoton a  yayin da yake...
Mutane 5 sun mutu A wani mummunan Hadarin mota da ya afku a jihar Delta

Mutane 5 sun mutu A wani mummunan Hadarin mota da ya afku a jihar Delta

Uncategorized
Hadarin Mota yayi saadin mutuwar mutane 5 a jihar Delta Rahotanni daga jihar Delta na nuni da cewa Wani mummunan hatsarin mota da ya afku a babban titin Asaba / Kwale A  jihar yayi sanadin salwantar rayukan mutane biyar tare da jikkata wasu da dama. Hatsarin, kamar yadda rahotanni suka labarto ya faru ne da yammacin ranar Lahadi, kusa da Ossisa, A karamar hukumar Ndokwa  dake gabashin jihar. Wani ganau, Joshua Nduka, ya shaida wa manema labarai cewa hatsarin ya faru ne lokacin da wata motar Mazda da ke tahowa daga hanyar falan daya ta yi karo da motar Toyota Hiace mallakar wani sanannen kamfanin sufuri a jihar. Lokacin da manema labarai suka tun tubi jami'in hukumar kiyaye hadura a jihar Mista Bakare Fatai Adesina ya bayyana cewa ba zai iya bada tabbacin wadanda suka salwanta a...
Wani Dan majalisa A Jihar Delta ya yi Allah wadai Da sace wasu malamai 2 A Jihar

Wani Dan majalisa A Jihar Delta ya yi Allah wadai Da sace wasu malamai 2 A Jihar

Tsaro
Memba mai wakiltar Mazabar Uvwie a majalisar dokokin jihar Delta, Hon. Solomon Ighrakpata ya yi tir da sace wasu malamai biyu da aka yi, A ranar Talata a makarantar sakandaren Ohorhe da ke karamar hukumar Uvwie a jihar. Honrabul Ighrakpata, wanda shi ne Mataimakin Babban Mai tsawatarwa na Majalisar, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici yana mai cewa hakan ka iya jefa malamai cikin zulumi a yayin da suke aikin koyo da koyarwa. Ya bukaci da Rundunar 'yan sanda data kokarta domin ceto wadanda aka sace. Idan za a tuna cewa wasu mahara dauke da bindiga sun sace wasu malaman makarantar sakandaren Ohorhe da ke karamar hukumar Uvwie a jihar Delta a ranar Talata. Inda aka rawaito cewa, wasu 'yan bindiga sun afka makarantar tare da yin garkuwa da Malamai 2 a makarantar.
Hatsarin mota yayi sanadin salwantan rayukan mutum 2 a jihar Delta

Hatsarin mota yayi sanadin salwantan rayukan mutum 2 a jihar Delta

Uncategorized
Wani mummunan hadarin mota da ya afku a karamar hukumar Isoko dake arewacin jihar Delta yayi sanadin mutuwar wasu fasinjojin babur mai kafa 2. Rahotanni sun bayyana cewa, Wata motar Bas da wata mota kirar Toyota sun yi sanadin mutuwar Diraban Babur tare da Fasinjan sa wanada hakan yayi sanadin mutuwarsu bayan da motacin biyu su ka murkushe mahayan. Jami'in hulda da Jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Onome Onovwakpoyeya ya tabbatar da Faruwar lamarin a yayin da yake tattaunawa da manema labarai a jihar. A cewar rahoton, bayan afkuwar lamarin wasu fusatattun Matasa sun bankawa motocin wuta.    
Mu a jihar Delta ba zamu daina biyan tsaffin gwamnoni fansho kamar yanda jihar Legas ta yi ba>>Gwamna Okowa

Mu a jihar Delta ba zamu daina biyan tsaffin gwamnoni fansho kamar yanda jihar Legas ta yi ba>>Gwamna Okowa

Siyasa
Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta ya bayyana cewa ba zasu bi sahun jihar Legas ba wajan hana tsaffin gwamnonin jihar Albashiba.   Gwamnan ya bayyana hakane a wajan wani taro da ya halarta.   Ya bayyana cewa, jiharsa na da dokar data ce a baiwa tsaffin gwamnonin ta Fansho shi kuma bazai canja wannan doka ba.   Yace jihar Legas ita tasan dalilin da yasa ta canja dokarta kuma ba zai so ya musu katsalandan ba. “There is an existing law in Delta State on what accrued to the governors and their deputies, that I don’t want to touch. “We are not thinking in that direction, my counterpart in Lagos may have reasons why he wants the law repealed but we in Delta don’t want to go into that. “I don’t want to comment on the decision of Lagos State G...
‘Yan bindiga a jihar Delta sun harbe wani Dan Banga

‘Yan bindiga a jihar Delta sun harbe wani Dan Banga

Tsaro
Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Sapele dake jihar Delta, inda wasu 'yan bindiga da ba'asan ko su waye ba su ka harbe wani Dan banaga mai suna Omile Chukwudi mai shekaru 38 da haihuwa. Rahotanni sun nuna cewa, Chukwudi ya gamu da ajalin sa ne, a yayin da ya ke kan aiki a kauyan su dake karamar hukumar Sapele a jihar. An dai kashe Mamacin ne da misalin karfe 12 da rabi na dare. Wata Majiya mai tushe ta shaida cewa, Dan bangar ya mutu ne a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta dawo wa gida. Da yake Amsa tambayoyi, Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar DSP Onome Onowakpoyeya ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya shaida cewa gawar mamacin tana Asbitin karamar hukumar.