
An samu ganin watan Dhul Hijja a sassa daban daban dake jahohin Najeriya
Hukumar dake kula da duban wata ta kasa ta bayyana cewa, a ranar talata sun samu rahoton ganin jin jirin watan Dhul Hijja wanda shine watan da al'ummar musulmai dake sassa daban daban a fadin Duniya ke yin aikin hajji kuma watan Dhul Hijja shine watan babbar sallah haka zalika shine wata na karshe a kalandar Musulunci.
Hukumar ta lasafta jahohin da aka tabbatar da ganin watan inda ya hada da Abuja, Jalingo, Lafiya, Illorin, Missau, da kuma Minna.
Kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta dake kafar sada zumunta.
https://twitter.com/moonsightingng/status/1285647507285053446?s=20
Ta ayyana ranar Laraba a matsayin daya ga watan Dhul Hijja.