fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Diego Costa

An yankewa dan wasan Atletico Madrid, Diego Costa hukuncin watanni shida a gidan yari

An yankewa dan wasan Atletico Madrid, Diego Costa hukuncin watanni shida a gidan yari

Wasanni
An kama tsohon dan wasan Chelsea da laifin zamba cikin amince wurin biyan kudin haraji kuma an yanke mai hukuncin watanni shida a gidan yari, Amma yanzu dan wasan ba zai je gidan yarin ba yayin da zai biya kudin fansa na euros 485,324 a cewar masu shari'a na kasar Spain. Costa ya yiwa kasar Spain zambar euros 900,000 bayan bai bayyana kudin daya biya ba na sama da euros miliyan hudu a lokacin daya koma Chelsea a shekara ta 2014, da kuma wata euros miliyan daya ta fannin hotuna. A safiyar yau Costa yaje wata kotu a garin Madrid domin ya tabbatar da yarjejeniyar amma mai magana da yawun kungiyar Atletico ya bayyana cewa Costa ya riga da ya biya kudin fansar tun a kwanakin baya kuma an janye maganar kaishe kurkuku. Diego Costa ya koma kungiyar Atletico Madrid a shekara 2017 kum...