
Barcelona 4-0 Osasuna, Lyon 1-3 Udinese,Lyon 3-0 Stade de Reims: Yayin da Messi ya bayyana rigar Nwell Old Boys domin tunawa da Maradona
Kungiyar Barcelona tayi nasarar lallasa Osasuna 4-0 a gasar La Liga ta yayin da Braithwaith da Antoine Griezmann suka ci mata kwallaye biyu tun kafin aje hutun rabin lokaci, shi kuma Lenglet ya samu rauni a wasan.
Philippe Coutinto yayi nasarar kara ciwa Barca kwallo guda kafin Messi yaci tashi kwallon wadda ya bayyana rigar kungiyar yarintar shi Nwell Old Boys domin tunawa da tauraron dan kasar shi Diego Maradona.
Ta bangaren Serie A kuwa kungiyar Udinese tayi nasarar lallasa Lazio 3-1 ta hannun Arslan, Pussetto da kuma Forestieri yayin da shi kuma Ciro Immobile ya ciwa Lazio kwallo guda.
https://www.instagram.com/p/CILkkcKlV2Z/?igshid=1it6gtr2p4k1d
A gasar Ligue 1, kungiyar Lyon tayi nasarar komawa ta biyu a saman teburin gasar nbayan data lallasa Stade de Reims 3-0 ta hannun Eka...