
Kotu ta baiwa EFCC nan da 3 ga watan Maris ta kawo Diezani Alison Maduekwe
Mai Shari'a, Ijeoma Ojukwu ta babbar kotun tarayya dake Abuja ta amince da bukatar EFCC ta kara daukar lokaci dan kawo tsohuwar minitar mai, Diezani Alison Maduekwe dan a mata shari'a kan zargin almubazzaranci da kudi.
A ranar 24 ga watan Yuli na shekarar 2020 ne kotun ta aikewa Diezani sammacen ta bayyana a gabanta amma ta kiya.
Lauyan EFCC, Farouk Abdullahi ne ya bayyana bukatar a gaban Alkali inda kuma aka amince masa.