
Ji Abinda Madam Korede ta gayawa DJ Abba bayan da yace bai san iya kajin da ya ci ba a Duniya
Tauraron mawakin Gambara, DJ Abba ya sha fada cewa shi Acici ne inda a lokuta daban-daban yakan yi raha da nuna yanda yake son Abinci.
A wannan karin ma irin haka ce ta faru inda ya bayyana a shafukansa na sada zumunta cewa Allah kadai yasan Kaji nawa yaci a Duniya.
Wannan magana tasa ta dauki hankulan masoyansa inda sukai ta bayyana ra'ayoyi mabanbanta akai.
Tauraruwar fina-finan Hausa, Madam Korede ta bashi amsar cewa, Gaskiya ba zasu Kirgu ba, Bakina Da Goro.