fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Doya

Gobara ta lalata kayyaki na miliyoyin naira a kasuwar Doya a yankin Filato

Gobara ta lalata kayyaki na miliyoyin naira a kasuwar Doya a yankin Filato

Tsaro, Uncategorized
Kayayyakin abinci da wasu kayayyaki masu daraja na miliyoyin nairori sun lalace sakamakon wata gobara da ta tashi a sanannen Kasuwar Doya ta Yamu a karamar hukumar Quaan Pan da ke jihar Filato a daren Lahadi. Wani mazaunin yankin, Alhaji Kabiri Buba, ya ce yawancin manoma da ‘yan kasuwa yanzu haka suna kirga asarar da suka yi. Buba ya ce, "Manoma da 'yan kasuwa sama da 100 matsalar ta shafa". Ya yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da ta taimaka wa manoma da ‘yan kasuwa. Dangane da lamarin, Sanatan da ke wakiltar Filato ta Kudu, Nora Dadu’ut a ranar Litinin ya yi ta’aziyya tare da babban basaraken yankin, Long Jan na Namu mai martaba, Alhaji Safiyanu Allahnana da sauran al’ummar musamman wadanda abin ya shafa. A baya dai, hutudole.com ya ruwaito muku yanda aka yi gob...