
Hukumar DPR ta bukaci Masu amfani da Gas na girki da su lura A wadannan lokuta na Hunturo
Hukumar Al'barkatun Man fetur ta kasa DPR ta yi kira tare da wayar da kan al'umma a jihar Sokoto kan kula da bin ka'ida na amfani da Gas na girki a lokutan Sanyi.
Hukumar ta bukaci Jama'a tare da masu sayar da Gas dasu mutunta ka'idojin yin amfani da Gas din a wadanan lokuta.
Sanarwar ta fito ne ta bakin Shugaban sashin hukumar Dake kula da shiyyar Sokoto da Jihar Kebbi Mista Musa Zarumai-Tambuwal wanda yayi wannan gargadin a yayin da yake zantawa da manema labarai A Sokoto.
Mista Zarumai-Tambuwal ya bukaci da Masu yin amfani da Gas a gurare daban-daban dasu ka hada da kasuwanni dasu kasance masu lura da kuma kula sakamakon lokuta ne da ake yawa yawan samun tashin gobara.