fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Dr. Abdullahi Umar Ganduje

Mutanen Kano Sun fi Bukatar Ilimi Fiye Da Gadar Sama>>Kwankwaso ga Ganduje

Mutanen Kano Sun fi Bukatar Ilimi Fiye Da Gadar Sama>>Kwankwaso ga Ganduje

Siyasa
Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya caccaki Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan shirin da yake yi na gina gadar sama da bashi a babbar hanyar da ke Hotoro a cikin garin Kano. Tsohon gwamnan ya caccaki Ganduje kan yadda ya samo bashin biliyan N20 don aikin, wanda a cewarsa alhakin gwamnatin tarayya ne ba gwamnatin jihar ba. Ku tuna cewa a cikin makon da ya gabata Gwamna Ganduje ya ziyarci Shugaba Muahammdu Buhari inda ya gabatar da samfurin hanyar matakai uku a kan hanyar Kano zuwa Maiduguri wacce za a sanya wa sunan shugaban kasa. Amma Kwankwaso a wata hira da Sashen Hausa na BBC na Juma’a ya ce, “Duk da cewa muna bukatar gadar sama a Kano, amma abin da mutane suka fi bukata a jihar shi ne ilimi. Suna buƙatar mayar da hankali ga yaranmu don su sami ilimi kuma s...
Shi kanshi Buhari bai fahimci zanen gadar da Gwamna Ganduje ya kai masa ba>>Kwankwaso

Shi kanshi Buhari bai fahimci zanen gadar da Gwamna Ganduje ya kai masa ba>>Kwankwaso

Siyasa
Tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa hotunan gadar da gwamna Ganduje zai gina a da ya kaiwa shugaba Buhari ba a zanasu da kyau ba.   Yace shi kanshi shugaba Buharin bai gane kan gadon hotunan ba. Kwankwaso ya bayyana hakane a hirarsa da BBChausa.   Ya kuma caccaki gwamna Ganduje da cewa kiwon Lafiya da Ilimi ya kamata ya baiwa muhimmanci ba gina gada ba, inda yace baya goyon bayan a yi rancen kudi har Biliyan 20 dan gina wannan gada. Yace gadar aikin Gwamnatin tarayya ce ba ta jiha ba.   A baya, hutudole.com ya ruwaito muku kayatattun hotunan gadar “Instead of Ganduje to go and see the president and ask him to do the bridge, because it is the responsibility of the federal government to do the flyovers connecting Kano ci...
Kayatattun hotunan sabuwar gadar da gwamna Ganduje zai gina a Hotoro

Kayatattun hotunan sabuwar gadar da gwamna Ganduje zai gina a Hotoro

Siyasa
Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da hotunan sabuwar gadar da zai gina a kwanar Hotoro, NNPC dake Kano.   Gadar zata kasancene akwai ta kasa data sama. Ya gabatar da hotunan gadar ne wanda za'a sakawa sunan shugaban kasa, Muhammadu Buhari ga majalisar zartaswa ta jihar dan amincewa.   Hadimin gwamnan,  Abubakar Aminu Ibrahim ne ya bayyana haka ta shafinsa na sada zumunta.  
Bidiyon Saka Dala a Aljihu Karyane>>Gwamna Ganduje

Bidiyon Saka Dala a Aljihu Karyane>>Gwamna Ganduje

Siyasa
Ɗaya daga cikin abubuwan da aka taɓo shi ne batun bidiyon da wata jarida ta fitar, inda ta yi iƙirarin cewa gwamnan Jihar Kano ne Abdullahi Ganduje yake karbar kuɗaɗen ƙasashen waje daga hannun wani mutum. Lamarin da ya janyo cece-ku-ce, ba ma a jihar Kano kawai ba, har ma da Najeriya baki ɗaya, abin da ya kai ga majalisar dokokin jihar kafa kwamiti domin binciken gaskiyar lamarin. Sai dai tun wancan lokaci gwamnan bai fito da kansa ya yi magana a kan zarge-zargen ba. Amma a lokacin tattaunawarsa da BBC ta awa guda, wani daga cikin al'ummar jihar da suka halarci dakin tattaunawar ya yi tambaya da bukatar ganin gwamnan ya yi bincike kan lamarin, kasancewar yana ƙoƙarin ganin an yaƙi ayyukan rashawa a jihar. A lokacin da ya yi tambayar, Kabir Dakata na Cibiy...
Da dumi-duminsa: An yi wa Gwamna Ganduje rigakafin Kurona

Da dumi-duminsa: An yi wa Gwamna Ganduje rigakafin Kurona

Siyasa
An yi wa Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje allurar rigakafin korona da ranar yau Alhamis.   An yi masa rigakafin ne ta AstraZenica a asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad da ke birnin Kano da karfe 2:49, inda likitansa Dr. Fakrudin Yahaya Muhammad ya yi masa.   Jihar Kano dai na cikin jihohin da suka karɓi kason allurar rigakafin daga cikin miliyan hudu da aka ba Najeriya.
An ci gaba da Shari’ar Bidiyon Dalar Gwamna Ganduje

An ci gaba da Shari’ar Bidiyon Dalar Gwamna Ganduje

Siyasa
Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a titin Miller na Unguwar Bompai, ta ci gaba da sauraron shari’ar bidiyon sun kuma daloli a cikin aljihu da ake zargin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje yana yi.   Tun a shekarar 2018 ne aka wallafa bidiyon zargin Ganduje yana sanya daloli a cikin aljihu wanda ake zargin cin hanci ne daga wani dan kwangila a Jihar, sai dai makarraban gwamnan suka ce bidiyon na bogi ne kuma an yi hakan ne don a bata wa gwamnatin suna.   Sai dai mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar wanda ya fitar da bidiyon ya dage a kan cewa sun inganta kuma babu coge a cikinsu.   A zaman kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a Sulaiman Baba Na Malam, a ranar Litinin, lauyan Jaafar Jaafar ya soki yadda masu wakiltar bangaren Ganduje suka ka...
Da dumi-duminsa: Kutu ta dakatar da Gwamna Ganduje daga shirya Mukabalar Malamai

Da dumi-duminsa: Kutu ta dakatar da Gwamna Ganduje daga shirya Mukabalar Malamai

Siyasa
Wata kotun majistiri mai lamba 12 da ke zaman ta a gidan murtala da ke Kano, ta dakatar da Gwamnatin jihar Kano daga yin mukabala tsakanin malam Abduljabbar da Malaman Kano.   A wata kara da lauya Barista Ma'auf Yakasai ya shigar yana neman a dakatar da mukabalar.   A yin zaman Kutun na yau Jumaa, mai sharia muhammad Jibrin ya bada umurni akan a dakatar da mukabalar har zuwa ranar 22 ga watan Maris da muke ciki na 2021.
Ganduje zai maka ‘masu yi masa batanci a kotu’

Ganduje zai maka ‘masu yi masa batanci a kotu’

Siyasa
Gwamnatin jihar Kano da ke Najeriya ta ce za ta gurfanar da duk wanda ya sake shiga gidajen rediyon “yana batanci ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje”. Kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba ne ya bayyana hakan. Ya ce mutane daban-daban suna shiga gidajen rediyo suna yin kalaman batanci ga gwamna na Kano abin da ya ce ba za su ci gaba da yin shiru a kai ba. Ya kara da cewa: “Muna tattaunawa da Kwamishinan Shari’a domin ganin mun gurfanar da duk wanda ya shiga gidajen rediyo yana bata mai girma Gwamna Ganduje. Mun gaji da irin wannan batanci”. Sai dai Malam Garba bai bayyana irin kalaman batancin da ya ce ana yi a kan gwamnan na jihar Kano ba. ‘Yan jam’iyyun adawa da masu sharhi kan lamuran yau da kulluma na kallon matakin a matsayin barazana ga ‘yancin fadar albarkacin baki wa...