fbpx
Friday, May 27
Shadow

Tag: Dr. Ahmad Gumi

Gumi Ya Jagoranci Shugabannin Addini Zuwa Gidan Obasanjo Kan Matsalar Tsaro

Gumi Ya Jagoranci Shugabannin Addini Zuwa Gidan Obasanjo Kan Matsalar Tsaro

Siyasa
Shahararren malamin addinin Islama, Sheik Ahmad Gumi, yanzu haka yana cikin ganawa da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a garin Abeokuta na jihar Ogun. Gumi, ya isa gidan tsohon shugaban wanda ke da dakin karatu na Olusegun Obasanjo (OOPL), Abeokuta, da misalin karfe 11 na safe, kuma kai tsaye ya shiga taron. Mai taimaka wa Obasanjo kan harkokin yada labarai, Kehinde Akinyemi, wanda ya tabbatar da haka ga Aminiya, ya ce wasu shugabannin addinai ma na halartar taron. “Ee, gaskiya ne. Shi (Gumi) yanzu haka yana ganawa da Baba tare da sauran shugabannin addinai, ”in ji Akinyemi. A kwanakin baya malamin ya hadu da kungiyoyin 'yan fashi a jihohin Zamfara da Neja don sasanta wadanda aka sace. Gumi ya roki gwamnati da ta yi wa ‘yan fashin afuwa, Wanda hakan ...
Dalilin da yasa har yanzu ‘yan Bindiga basu sako daliban Kaduna ba>>Sheikh Gumi

Dalilin da yasa har yanzu ‘yan Bindiga basu sako daliban Kaduna ba>>Sheikh Gumi

Tsaro
Shehin malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa dalilin da yasa 'yan Bindiga basu sako daliban Kaduna ba, Saboda dokar shugaban kasa, Muhammadu Buhari ce ta harbin duk wanda aka gani da Bindigar AK47.   A ranar 11 ga watan Maris ne dai aka sace daliban, kusan makonni 2 da suka gabata kenan.   Malamin yace a shiga dajin da yayi, ya tattauna da kusan kaso 80 na shuwagabannin 'yan bindigar, kuma in banda rashin hadin kan wasu shugabannin gwamnati, da ya gana da duka shuwagabannin 'yan bindigar. Yace ta hanyar 'yan Bindigar da ya tattauna dasu a baya, an gano shugaban 'yan Bindigar da ya sace daliban Kaduna amma kuma bai taba halartar taron sulhu ba.   Yace kuma matsalar dokar da gwamnati tasa ta harbin duk wanda aka gani da Bindiga yasa ba...
Sheikh Gumi ya bayyana dalilin da yasa ‘yan Bindiga ba zasu iya aje makamansu ba

Sheikh Gumi ya bayyana dalilin da yasa ‘yan Bindiga ba zasu iya aje makamansu ba

Uncategorized
Shehin malamin addinin Islama,  Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa idan gwamnati bata baiwa 'yan Bindiga tabbacin tsaron rayuwarsu ba, da wuya su ajiye makamai.   Yace sun shiga daji kuma sun nunawa wadannan Fulani cewa za'a sauraresu, yace kuma Fulanin a shirye suke su ajiye makamansu.   Yace suna da matsaloli irin nasu, baau da ilimi, kuma babu wata kasa da take son zaman lafiya da ci gana da zata bar mutanenta cikin jahilci.   Yace idan dai da gaske gwamnati take ya kamata a yiwa wadannan Fualni Afuwa kamar yanda akawa Tsageran Naija Delta. Ahmad Gumi, an Islamic cleric, says if bandits are not assured of their safety and rehabilitation, they will not let go of their arms. Gumi made the comment on Wednesday during a virtual event hosted by the Nati...
Satar dalibai ya fi sauki fiye da kashe gaba dayan mutanen kauye>>Sheikh Gumi

Satar dalibai ya fi sauki fiye da kashe gaba dayan mutanen kauye>>Sheikh Gumi

Tsaro
Shehin malamin addinin Islama,  Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa satar dalibai da a yanzu 'yan Bindiga suke yi yafi sauki fiye da yanda a baya suke shiga gari su kashe gaba dayan jama'ar garin.   Yace wanda suka sace daliban Jangebe na yanzu wasu 'yan Bindiga ne dake kokarin nuna rashin jin dadinsu saboda Gwamnati ta ki sakasu cikin wanda take sulhu dasu.   Yace kuma hakam ya nuna cewa wa'azin da yakewa 'yan Bindigar na aiki, saboda a baya sukan kashe jama'ar gari gaba daya amma yanzu suna daukar mutanene ba tare da sun ji musu rauni ba.
Zan kai ziyara Kagara inda aka sace dalibai>>Sheikh Gumi

Zan kai ziyara Kagara inda aka sace dalibai>>Sheikh Gumi

Tsaro, Uncategorized
Shehin Malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa zai kai Ziyara Kagara ta jihar Naija inda aka sace daliban makarantar Sakandare.   Ya bayyana hakane kamar yanda Daily Trust ta ruwaito inda yace yana kan hanyarsa ta zuwa Kebbi ne amma ya tsaya dan su gana da Gwamna Abubakar Bello.   Ya bayyana cewa sun gana da Gwamna Bello sosai akan matsalar tsaron. “The governor and I spoke on several ways to deal with insecurity in a holistic manner and find solutions to the insecurity problem in the state,” he said.
Da Duminsa:Shekau ya saki sabin Sautin Muruya inda yawa Sheikh Dr. Ahmad Gumi Barazana

Da Duminsa:Shekau ya saki sabin Sautin Muruya inda yawa Sheikh Dr. Ahmad Gumi Barazana

Uncategorized
Shugaban Boko Haram,  Abubakar Shekau ya saki sabon sautin Murya inda yakewa babban malamin addinin Islama dake jihar Kaduna, Sheikh Dr. Ahmad Gumi Barazana.   A hirar da yayi da BBChausa, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa 'yan ta'adda na amfani da Fulani saboda rashin cikakken Ilimin Addini suna tada zaune tsaye, wannan ne yasa ya shiga daji dan ya karantar da Fulanin.   Saidai a wata murya data bayyana a jiya, Talata da ta yi ikirarin cewa Shugaban Boko Haram,  Abubakar Shekau ne ta musanta cewa tana amfani da Fulani wajan aika-aikar ta inda kuma ya bayyana gargadi ga Shehin Malamin kan ya daina musu irin wancan zargin.   Shekau din ya bayyana cewa, basa amfani da kowabe irin mutane suna aikata laifuka amma sun san cewa akwai masu amfani da sunansu suna a...
Ishara Allah Ya Yi Wa Gwamnatin Nijeriya Game Da Rikicin SARS, Wannan Somin Tabi Ne>>Sheikh Gumi

Ishara Allah Ya Yi Wa Gwamnatin Nijeriya Game Da Rikicin SARS, Wannan Somin Tabi Ne>>Sheikh Gumi

Uncategorized
Fitaccen Malamin addinin musulunci a Nijeriya kuma kwararren likita Sheikh Dr Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana cewa tashin-tashinar da ta faru ba komai ba ne illa ishara da Allah ke yi wa shugabannin Najeriya kan kusa-kuran da su ke aikatawa, kuma muddin ba su gyara ba wannan zai zama kadan daga abinda za su gani zuwa gaba.   "Ba zai yuwu ana kashe rayukan mutane ana salwantar da su ba, mutane na cikin tsananin yunwa da tsadar rayuwa ba, amma a danne bakin mutane a hana su yin korafi, sanda 'yan Arewa su ka fara zanga-zangar Lumana kama shugannin zanga-zangar aka yi aka tsoratar da mutane" Cewar shehin Malamin.   " Ko shekaranjiyar nan a Zamfara an kashe mutum ishirin da biyu, ban jima da dawowa daga Sokoto ba suna fad'a min mutum saba'in da tara aka kashe, kullum ne s...
Mustahabbi Ne A Yi Zanga-zangar Lumana Da Nufin Kawo Sauyi Ga Al’umma>>Dakta Ahmad Gumi

Mustahabbi Ne A Yi Zanga-zangar Lumana Da Nufin Kawo Sauyi Ga Al’umma>>Dakta Ahmad Gumi

Uncategorized
Fitaccen Malamin addinin musulunci kuma kwararren likita a Nijeriya Sheikh Dr Ahmad Gumi ya yi tsokaci game da Zanga-zangar lumana da matasa ke yi bisa matsalar tsaro a arewacin Nijeriya a matsayin kyakkyawan abu da musulunci ke so a yi. Malamin ya ce duk wata zanga-zanga da za ta kawo wa al'umma mafita ko sauyi a rayuwarsu mustahabbi ce a addininance wacce aka so a aiwatar da ita.   "Zanga-zanga idan ta babin mu'amalah ce da siyasah, to dole ayi tafsili. In tanada amfani a mahangar shariah to hukuncin ta yakan fada akan hukunce hukuncen shariah na wajibci, ko mustahabbi ko Halas ko makaruhi ko Haram." In ji Malam Gumi.   Ya kara da cewa " Zanga-zangar da zata kawo rarrabuwar kan jamaah ko salwantar dukiya ko rayuka haramun ce magana guda.   Zanga-z...
Sheikh Ahmad Gumi ya bada shawarar a Bude Boda dan shigo da Abinci

Sheikh Ahmad Gumi ya bada shawarar a Bude Boda dan shigo da Abinci

Uncategorized
Ya Kamata Buhari Ya Bude Boda A Daidai Wannan Lokaci Da 'Yan Nijeriya Ke Cikin Mawuyacin Hali Na Tsadar Abinci, Cewar Sheik Ahmad Gumi Sheik Gumi wanda ya bayyana hakan a wani sautin murya da BBC ta fitar, ya kara da cewa akwai kasashe da dama da idan aka bude boda za su shigo da abinci Nijeriya wanda hakan zai sa kayan abinci ya yi arha, saboda a wasu kasashe abinci har neman lalacewa yake saboda sun rasa inda za su kai su sayar.
YA KAMATA MU NEMI YAFIYAR SHEIKH DR AHMAD GUMI, DUK ABINDA YA FADA KAN MULKIN BUHARI YA TABBATA>>DATTI ASSALAFIY

YA KAMATA MU NEMI YAFIYAR SHEIKH DR AHMAD GUMI, DUK ABINDA YA FADA KAN MULKIN BUHARI YA TABBATA>>DATTI ASSALAFIY

Siyasa
Hakika a yanzu ne nake kara fahimtar lamarin Sheikh Dr Ahmad Gumi game da ra'ayinsa a kan siyasa, bana tare dashi a kan wasu fahimtarsa na addini sam, amma a kan siyasa kam yanzu na fahimce shi sosai. Gaskiya ya fada, kuma gaskiya ya hango mana, kuma ya gina maganarsa ne a kan abinda marigayi Sheikh Albaniy Zaria ya gina cewa shugaba Buhari mai gaskiya ne, da wahala ya iya shugabancin mutane marassa gaskiya, matsalar shine su waye zasu taya shugaba Buhari mulki? shin masu gaskiya ne? Dr Gumi ya ce shugaba Buhari tsufa ya kama shi, ya yi shekaru cikin hidima wa tsaron kasa a aikin soja, yana bukatar hutu ne amma mutanen nan 'yan jari hujja suka je suka kinkimo shi don mai gaskiya ne suka kafa shi don biyan bukatar kansu. Akwai lokacin da Dr Ahmad Gumi yake raddi game da yadda EFC...